Yanzu sojojin Najeriya na samun Naira 100,000 a wata – Minista

Army Army

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce yanzu sojojin Najeriya na samun albashi akalla Naira 100,000 a wata bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi sabon garambawul a fannin jin dadinsu.

Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da News Central a ranar Laraba, kafin a watsa shirin a shirin NC Exclusive ranar Juma’a.

Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Kasar, ya kuma ce duk da inganta jin dadin ma’aikata, har yanzu ba a ba rundunar tsaro isasshen kudi ba.

Da aka tambaye shi ko kasafin kudin tsaro na yanzu ya isa, ministan ya amsa da cewa, “Bai isa ba.”

Sai dai ya ce Gwamnatin Tarayya ta inganta albashin sojoji sosai.
“Lokacin da suka fara, soja yana karban N49,000 a wata, mun yi kokari sosai yanzu suna karban Naira 100,000,” in ji shi.

Ministan ya kuma ba da shawarar a sanya hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, yana mai cewa ana bukatar daukar tsatsatsauran hukunci domin dakile yawaitar satar mutane a fadin kasar.

“Ina tunanin ya kamata mu yi haka. Dole ne a sami tsoratarw, dokoki ba su da karfi, shi ya sa mutane ke cin gajiyar hakan. Idan da sun san da zarar ka aikata laifi, za a hukunta ka,” in ji Musa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here