Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta kama tare da tsare Sakataren Gwamnatin Jihar Osun, Teslim Igbalaye, tare da wasu mutane 5 bayan sun kai samame a gidansa da ke Osogbo.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Abiodun Ojelabi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ya ce daya daga cikin wadanda aka kama a gidan, Oladele Abiodun, na cikin jerin mutanen da ‘yan sanda ke sanya ido akansu kan zargin aikata laifuka.
A cewar ‘yan sanda, an gudanar da wannan aiki ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addar da ake zargi na boye ne a wani wuri a Osogbo.
Wadanda aka kama sun hada da Teslim Igbalaye mai shekara 47, Akande Taiwo 60, Oladele Abiodun 38, Adeyemo Lukman 45, Olaoye Muftau 50 da Aderemi Musliu mai shekara 40.
‘Yan sanda sun ce jami’ansu sun kwato kudi Naira 4,810,500, Katin Zabe guda 2, rijistar masu zabe ta mazabu 1 zuwa 15, kwamfuta ta kirar Dynabook, na’urar kwafar abu da kuma na’urar buga takardu a yayin samamen.
A cewar Ojelabi, an ajiye dukkan kayan da aka kwato kuma ana gudanar da bincike na kimiyya a matsayin wani bangare na ci gaba da bincike.
Ya ce kwato kudin da rijistar masu zabe ya haifar da damuwa kan yiwuwar aikata laifukan zabe da sauran miyagun ayyuka.
‘Yan sanda sun lissafa laifukan da ake bincikarsu da suka hada da zargin sayen kuri’a bisa Sashi na 121 na Dokar Zabe 2022, hada baki don aikata laifi, boye ko kare wanda ake nema da ‘yan sanda da duk wasu laifuka da za su iya fitowa daga binciken.
“An kwato kudi da rijistar da ke dauke da bayanan masu zabe, wannan ya haifar da damuwa mai tsanani kan yiwuwar aikata laifukan zabe da sauran laifuka,” in ji sanarwar.
Rundunar ta kara da cewa an kara karfafa bincike don gano inda aka samu kudaden da aka kwato da kuma manufar amfani da su, gano duk mutanen da ke da hannu cikin kayan da aka kwato da kuma gano girman duk wata kungiyar laifuka.
Ya jaddada cewa wadannan zarge-zarge na da tasiri kan tsaron jama’a, gudanar da adalci da kuma sahihancin tsarin dimokradiyya.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Jihar Osun ta zargi ‘yan sanda da kutsawa gidar Sakataren Gwamnatin Jihar ba tare da samun takardar izinin bincike ba.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Ilimin Jama’a, Kolapo Alimi, ya sanya hannu, gwamnatin jihar ta zargi jami’an ‘yan sanda da kama mutanen da aka samu a gidan yayin samamen.
Alimi ya kara da cewa hadaddiyar tawagar ‘yan sanda ce ta kai samamen gidar, ana zargin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Ayyuka ne ya jagorance su.












































