Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya amince da ranar 12 ga watan Afrilu don gudanar da babban taron jam’iyyar na shiyyar Kudu maso Kudu da aka dage tun farko.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ologunagba ya ce, NWC ta kuma amince da sauya ranar taron ta na shiyyar Kudu-maso-Yamma da Arewa ta Tsakiya daga ranar 22 ga Maris zuwa 12 ga Afrilu.
Ya ce za a gudanar da taron na shiyya a lokaci guda a Fatakwal na shiyyar Kudu maso Kudu; Ibadan, na shiyyar Kudu-maso-Yamma da Jos, na shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Karanta: PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa
Kakakin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa za a zabi shugabannin zartarwa da tsofaffin ‘yan majalisu na shiyyoyi daban-daban a majalissar dokokin, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
Ya kuma bukaci dukkan masu son tsayawa takara, shugabannin PDP, masu ruwa da tsaki na shiyyoyin su, INEC, hukumomin tsaro da kafafen yada labarai da su lura da ranakun da za a gudanar da taron shiyya domin samun jagoranci yadda ya kamata. (NAN)