Jam’iyyar APC ta dakatar da sanatan da ke wakiltar yankin Kogi ta Gabas, Jibrin Isah Echocho, bisa zargin ayyuka da suka saba wa muradun jam’iyyar.
An yanke wannan hukuncin ne bayan matsayar da Kwamitin Zartarwa na Mazabarsa ta Odu Ward 2 a Karamar Hukumar Dekina ta jihar a taron da suka gudanar a ranar 26 ga Mayu 2026, wanda aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis a Lokoja.
A cikin wasikar dakatarwar da Shugaban Mazabar, Shaibu Mohammed da Sakatare, Kabiru Mohammed, tare da sauran shugabanni suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta zargi sanatan da “gudanar da ayyukan adawa da jam’iyya na tsawon lokaci”, tana mai zargin cewa burin sanatan wani bangare ne na kokarin cimma “burin wa’adi na uku na kansa”, maimakon muradun jam’iyyar a matakin mazaba da yanki da jihar.
Shugabannin mazabar sun ci gaba da zargin Echocho da cewa ya na yin aiki akasin muradun APC duk da ya amfana da dandalinta tsawon shekaru takwas.
A wani bangaren, Kungiyar KEPF ta karyata dakatarwar da ake zargin an yi wa sanatan, tana mai cewa “bata kan ka’ida, ba kuma ta da tushe, siyasa ce”.
Mai magana da yawun kungiyar, Kamared Musa Ibrahim, ya bayyana wannan zargi da kokarin abokan hamayyar sanatan don bata sunan sanatan.
A ’yan makonnin baya, Sanata Echocho ya yi zargin cewa gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar a yankin Kogi ta Gabas ya sabawa ka’idojin jam’iyya da dokokin zabe, sannan ya shigar da kara ga Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) kan zaben da Joseph Erico Ameh ya lashe.












































