Jose Mourinho ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru uku don zama sabon kocin Real Madrid.
Ba za a bayyana shi a hukumance ba sai bayan zaben shugaban kungiyar, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga Yuni.
Duk da haka, kwantaragin kocin mai shekaru 63 zai kasance ne kawai idan shugaban kungiyar na yanzu, Florentino Perez, ya ci gaba da kasancewa kan mukamin shi.
Perez ya sanar da zaben ne a wani taron manema labarai na musamman a farkon wannan wata, inda ya soki ’yan jarida da La Liga kuma ya yi magana kan “ wani shiri da ake yi ba bisa ka’ida ba” a kan sa.
Mutumin mai shekaru 79 ya kasance kan mulki tun 2009 kuma ya taba zama shugaba tsakanin shekarar 2000 zuwa 2006 amma ya fuskanci shekaru biyu ba tare da lashe kofuna ba.












































