‘Yar Najeriya Maryam Dan’azumi ta lashe gasar Alqur’ani ta duniya a Saudi Arabia

Danazumi 713x430

Maryam Ibrahim Dan’azumi, ‘yar asalin Jihar Gombe ta zama zakara a gasar Karatun Alqur’ani ta Duniya ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Masarautar Saudi Arabia.

Maryam, daliba ce a Makarantar Alqur’ani ta Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation dake Herwagana Quarters, Gombe, ta wakilci Najeriya a wannan gasa mai daraja ta duniya, inda ta yi takara a bangaren karatun Alqur’ani ta Hizifi 60 tare da tajweed da tafsiri.

Ta zarce ‘yan takara daga kasashe da dama har ta zo ta yi nasarar zama ta daya, inda ta samo wa Jihar Gombe da Najeriya girma da kyakkyawan suna.

Nasarar da ta samu ta kasance ta tarihi musamman saboda wannan shi ne karo na 46, karona farko da aka baiwa mata damar shiga cikin shekaru 46 da aka fara gudanar da gasar, wanda hakan ya sa nasarar Maryam ta fi fice.

A cikin wata sanarwa da Ismaila Uba Misilli, Daraktan Yada Labaran Gwamnatin Gombe ya fitar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya Maryam, iyalinta, malamanta da al’ummar musulmi na Jihar Gombe murna, inda ya ce wannan nasara alfahari ne mai girma ga Gombe da Najeriya.

Gwamnan ya ce nasarar Maryam ta nuna muhimmancin ladabi, jajircewa da sadaukarwa ga karatu, sannan ta bayyana baiwa da hazakar da matasa ke da ita a Jihar Gombe.

“Ina alfahari sosai da nasarar ‘yarmu a matakin duniya. Nasar Maryam misali ne na nagarta da gadon ilimi mai kyau na Jihar Gombe. Nasararta ta samu alfahari ba ga Gombe kadai ba, har ma ga Najeriya baki daya,” in ji shi.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kara da cewa wannan nasara za ta karfafa sauran matasa, musamman ‘yan mata, su nemi nagarta don su yi fice a fannin da suka zaba.

Ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa ci gaban ilimi ga matasa, ciki har da ilimin Alqur’ani da na addini, wanda ya ce yana da muhimmanci wajen gina ladabi, kyawawan dabi’u da zama dan kasa na gari.

Zuwan Maryam gasar duniya ma wani labari ne mai zaman kan shi, ta zo ta farko a matakin Ƙaramar Hukuma a Gombe, sannan ta farko a matakin Jihar Gombe, sannan ta farko a matakin Kasa, kafin ta wakilci Najeriya a gasar duniya da aka gudanar a Makka, Saudi Arabia.

Gwamnan ya ce yana sa ran tarba da ba ta lambar yabo da kansa da zarar ta dawo Najeriya. Ya ce baiwa irin wadannan mutane lambar yabo zai karfafa su wajen ci gaba da neman nagarta, kuma zai zaburar da sauran matasa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yaba da gudunmawar da Makarantar Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation ta bayar wajen nasarar Maryam.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here