An nada Farfesa Adamu Ahmed a matsayin sabon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
A cewar sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar ya fitar ranar Laraba, ya ce Farfesa Adamu Ahmed ya maye gurbin Farfesa Kabir Bala.
Sa safiyar wannan rana ne aka sanar da nadin a yayin taron majalisar zartarwar jami’ar karo na 209, wanda shugaban kungiyar Mahmud Yayale Ahmed ya jagoranta.
Karin labari:BUK ta karawa Ministan Ilimi, Suleiman Yaradua, Muhammad Umar da wasu 63 matsayi zuwa farfesoshi
Farfesa Ahmed, malami ne a sashen tsara Birane, kuma a baya ya yi aiki a matsayin darakta na hukumar ci gaban Jami’a.
Sannan kuma shi ne Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta tarayya ta Kano.
Masu ruwa da tsaki sun yi maraba da nadin nasa, inda suka bayyana shi a matsayin gogaggen malami kuma mai kwarewa a fannin gudanarwa.