‘Yan Najeriya dake samun 60,000 sun fi wasu da suka yi hijira zuwa ketare jin dadi – Bwala

Daniel Bwala sabo 750x430

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Manufofi, Daniel Bwala, ya ce dan Najeriya da ke samun Naira 60,000 a wata ya fi wasu yan kasar da dama da suka koma kasashen ketare shekaru biyar da suka wuce, yana mai cewa tsadar rayuwa a ketare ta sanya rayuwa ta yi wa da yawa daga cikinsu wahala.

Yayi wannan maganar ne a shirin The Morayo Show, inda ya ce yan Najeriya da yawa da ke Burtaniya wadanda suka bar kasar don neman dama sun fi yin ayyukan da bai dace da takardun karatunsu ba yanzu.

“Wasunku da ke tunanin suna fama a Najeriya, kun fi abokan aikinku da suka yi bar kasar shekaru biyar da suka wuce,” in ji Bwala.

Da yawa daga cikin masu digiri a yanzu suna aiki a gidajen aikatau da dakunan ajiya, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani nau’in cin zarafi.
“A ganina, wannan bauta ce ta zamani,” in ji shi.

A cewarsa, duk da cewa da yawa daga cikinsu na samun tsakanin Yuro 2,600 zuwa 2,800 a wata, mafi yawan kudaden suna tafiya ne kan haya, lissafin ruwa da wuta, intanet, sufuri da ciyarwa, dan abin da ya rage ba ya da yawa.
“A karshe abin da ya rage maka ba ya da yawa. Don haka ana tilasta maka ka yi aiki biyu ko uku,” in ji shi.

Bwala ya ce mutumin da ke samun Naira 60,000 a Najeriya zai iya dogaro da goyon bayan iyali da abokai, ba kamar yawancin yan Najeriya da ke zaune a waje ba.
“Wanda ke samun ₦60,000 na iya samun goyon baya daga iyali da abokai, yayin da mutane da yawa a waje babu wanda za su dogara da shi,” in ji shi.

Bwala ya kuma kare shirye-shiryen tallafi na zamani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gwamnati ta bullo da matakai don rage kudin kiwon lafiya.
“Shugaba Bola Tinubu ya bullo da tallafin kashi 50 cikin 100 kan jiyya dialysis a asibitocin gwamnatin tarayya, sannan an sanya haihuwar ciki ta hanyar tiyata kyauta a asibitocin gwamnati,” in ji Bwala.

Ya kara da cewa gwamnati na shirin fadada tallafin kiwon lafiya zuwa wasu ayyukan likita da magunguna yayin da kudade suke kara samuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here