Amurka za ta daina aikin bada biza a Abuja, Ouagadougou, da wasu birane 23 na Afirka

US Visa 750x430

Amurka ta sanar dawani babban sauyi a fannin aikin bada biza a fadin Afirka, inda a ofishin jakadancinta na Abuja da wasu ofisoshi 24 na diflomasiyya za a daina bayarwa daga ranar 1 ga Agusta, 2026.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce wannan sabon tsarin na mayar da aikin zuwa cibiyoyi na yanki na daga cikin kokarin kara karfafa tsaron kasa, rage asara ga gwamnati, da tabbatar da daidaiton bincike, tantancewa da yanke hukunci.

A cewar sanarwar da Ma’aikatar ta fitar, gwamnatin Shugaba Trump na ba da fifiko ga Amurka da ‘yan Amurka ta hanyar sake tsara ayyukan ofisoshin waje domin cimma manufofin Amurka yadda ya kamata da inganci.

“Ma’aikatar Harkokin Waje na ci gaba da nazarin ayyukanta na wajen kasar domin ciyar da manufofin Amurka gaba yadda ya kamata da inganci, wanda ya hada da tsarin biza da ke kiyaye ka’idojin tsaro mai karfi da kuma daidaita albarkatu da karfin aiki da bukatun kasar Amurka.

“Babban fifikon gwamnatin Trump shine tsaro da amincin ‘yan Amurka, kuma Ma’aikatar Harkokin Waje za ta ci gaba da aiki ga ‘yan Amurka a ofishin jakadanci da taimaka musu a ofisoshin diflomasiyya a fadin duniya,” in ji sanarwar.

Sauran ofisoshin da abin zai shafa sun hada da Asmara, Bamako, Banjul, Brazzaville, Bujumbura, Conakry, Cotonou, Durban, Freetown, Gaborone, Harare, Juba, Libreville, Lilongwe, Lusaka, Maputo, Maseru, Mbabane, N’Djamena, Niamey, Nouakchott, Ouagadougou da Windhoek.

Ma’aikatar ta jaddada cewa wannan sauyi ba zai canza yanayin aiki na kowanne ofishin jakadanci ba, ko kuma muhimman ayyukan da suke gudanarwa a madadin ‘yan Amurka.
Ta kuma bayyana cewa wandannan sabbin manufofin ba su shafi kowacce biza ta Amurka da ke aiki yanzu ba.

An bayyana cewa rukunonin bizar bakin haure da za a sake tsara wa sun hada da dangi na kusa (IR), zabin dangi (FP), bizar aiki (EB), bizar saurayi ko budurwa mai shirin aure (K), daukar yaro (adoptions), bizar caca da kuma shari’o’in dangi na ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka (V92/V93).

Ma’aikatar ta ce sun riga sun gwada mayar da aikin bizar zuwa cibiyoyi a wasu kasashen Afirka da Turai, kuma ya samu nasara.

Legas da wasu ofisoshi 19 za su ci gaba da aiki.

Sai dai Ma’aikatar ta ce za a ci gaba da aiki na yau da kullum na bada bizar a ofisoshin jakadanci da konsulat na Amurka a Legas, Abidjan, Accra, Addis Ababa, Cape Town, Dakar, Dar-Es-Salaam, Djibouti, Johannesburg, Kampala, Kigali, Kinshasa, Lome, Luanda, Malabo, Monrovia, Nairobi, Port Louis, Praia, da Yaoundé.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here