Shuagaban karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi, Honorable Muhammed Danasabe, ya rasu.
Bayanai sun tabbatar da cewa Danasabe ya rasu ne a asibiti da misalign karfe 4 da mintuna 30 na asubahin ranar Juma’ar nan.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mutuwar Shugaban karamar hukumar ta Lokoja na zuwa ne yayin day a rage kwana guda a kada kuri’a a zaben gwamnan Jihar ta Kogi, da aka shirya gudanarwa a ranar asabar 11 ga watan Nuwambar, shekarar da muke ciki ta 2023.
Iyalan marigayin sun ce za’a yi jana’idar sa kuma a binne shi a makabartar Musulmi dake Unguwan Kura bayan idar da sallar Juma’a.
Marigayin wanda ya kasance shugaban karamar hukumar Lokaja, ya rasu ya bar mahaifiyarsa, da matar sa daya da kuma Yara.