EFCC ta ayyana tsohuwar ministar jin kai Sadiya Farouq a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo

images 39

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ayyana tsohuwar Ministar Jin Kai, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wanda ake nema kan zargin hada baki da aikata laifi, cin zarafin mukami, da karkatar da dukiyar jama’a.

Hukumar yaki da cin hanci ta wallafa sanarwar neman ta ne a shafinta na intanet a ranar Asabar.

A cewar sanarwar EFCC, Farouq mai shekaru 52 ‘yar asalin Jihar Zamfara ce, kuma adireshinta na karshe da aka sani shi ne EN 008, Okpo River, off Agulu Street, Maitama, Abuja.

Sanarwar, wadda Shugaban Sashen Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu, ta bukaci al’umma masu bayanin inda take da su tuntubi hukumar.

Sanarwar EFCC ta ce, “Jama’a ana sanar da ku cewa Sadiya Umar Farouq, wadda hotonta ke bayyane a sama, hukumar EFCC na nemanta kan wani al’amari na zargin hada baki da aikata laifi, cin zarafin mukami, da karkatar da dukiyar jama’a.”

Hukumar ta umarci duk wanda ke da bayani mai amfani da ya tuntubi ofisoshinta da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Port Harcourt, ko Abuja, ko ya kira 08093322644, ko ya aika sako ta info@efcc.gov.ng, ko ya kai rahoton ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Farouq ta yi aiki a matsayin Ministar Harkokin Jin Kai, Bala’i da Raya Al’umma a karkashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga 2019 zuwa 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here