An fara aikin farfado da cibiyar ruwa ta Guzu-Guzu bayan shekaru hudu ba ta aiki a kano

FB IMG 1783467814726 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta farfado da cibiyar ruwa ta Yankin Guzu-Guzu bayan shekaru fiye da hudu ba ta aiki, ta dawo da aikin samar da ruwa mai karfin lita miliyan 7.2 a kowace rana da ke hidima ga Kananan Hukumomin Kabo da Rimin Gado.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir M. Hashim, ne ya sanar da wannan ci gaba a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Talata. Ya ce dawo da aikin na daga cikin manyan nasarorin gwamnatin jihar na kokarin inganta samun ingantaccen ruwan sha mai tsafta.

Ya ce al’ummomin da ke cikin yankin da cibiyar ruwan ke kaiwa za su fara samun ruwan daga Laraba 8 ga Yuli, yayin da aka fara gwajin da kaddamarwa.

A cewar kwamishinan, gyaran da aka yi ya hada da sanya sabon janareta mai karfin 800 kVA, gyara famfuna hudu na ruwa, gyara bangaren wuta, ofisoshin ma’aikata da wuraren tsaro domin dawo da wajen zuwa cikakken yanayin aiki.

Ya bayyana cewa samar da ruwan mataki ne daga cikin tsarin gwaji da kaddamarwa, yana mai cewa za a ci gaba da aiki har sai an dawo da wajen zuwa cikakken matakin da zai biyan bukatar mazauna yankunan da ke amfana daga shi.

Hashim ya ce dawo da aikin na Guzu-Guzu na nuna aniyar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sake farfado da muhimman kayayyakin aikin ruwa a fadin jihar.

“Gwamnatin Mai Girma, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na da aniya ta musamman wajen sake farfado da dukkanin cibiyoyin ruwa a yankuna 19 dake Jihar Kano domin tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha mai tsafta ga al’ummarmu baki daya,” in ji kwamishinan.

SolaceBase ta bayyana cewa a cikin makonnin nan, Gwamnatin Jihar Kano ta kara kaimi a kokarinta na dawo da aikin samar da ruwa ta hanyar gyara kayan aikin ruwa a fadin jihar.

A baya-bayan nan gwamnati ta fara gyaran cibiyar ruwa ta yankin Joda bayan shekaru bakwai bata aiki, sannan ta kuma sake fara tura ruwan da aka tace daga matatar ruwa ta Challawa zuwa madatsar ruwa ta Goron Dutse.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here