Gwamnatin Edo Ta Bayyana Bacewar Motoci Sama Da 200

Edo Gov. Monday Okpebholo 750x430

Shugaban kwamitin da Gwamna Okpebolo ya kafa domin kwato motocin gwamnati, Mista Kelly Okungbowa, a ranar Juma’a ya bayyana cewa sama da motoci 200 ne suka bata.

Ya ce cikin sa’o’i 24 ne kwamitin ya kwato motoci uku a wani gida mai zaman kansa a Benin.

Okungbowa, wanda ya zanta da manema labarai kan nasarar da kwamitin ya samu, ya ce a cikin sa’o’i 24 an kwato motoci uku da suka hada da kirar Hilux guda daya da kuma motocin Toyota Hiace guda biyu.
Ya bayyana cewa a daya daga cikin motocin Toyota Hiace, kwamitin ya kwato wasu kayan agajin da aka so rabawa mutanen Edo.

Shugaban ya kara da cewa abubuwan da suka taimaka sun hada da buhunan garri da shinkafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here