Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace ‘yan uwa uku na tsohon Editan Aminiya, Malam Ahmed Ajobe.
Wadanda abin ya shafa sun hada da kanwar Mista Ajobe, Halimtu-Sadiya Tahir.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Lokoja a ranar Juma’a.
A cewar Aya, tuni jami’in ‘yan sanda reshen yankin da ke kula da yankin ya tura mutanensa yankin domin tabbatar da ceto wadanda lamarin ya shafa.
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da su ne a ranar Alhamis a kan titin Ankpa-Adoka-Markudi, yayin da suke dawowa daga wata kasuwa da ke kusa da garin Awo, cikin karamar hukumar Ankpa ta jihar.