Tsohon gwamnan Kano, Abubakar Rimi, ya cika shekaru 13 da rasuwa

1680603344421
1680603344421

Tsohon gwamnan Kano, Abubakar Rimi, ya cika shekaru 13 da rasuwa. Ya rasu a ranar 4 ga Afrilu, 2010.

An haifi marigayin a shekarar 1940 a karamar hukumar Sumaila a nan Kano.

Yayi gwamnan Kano daga watan Oktoban 1979 zuwa Mayun 1983.

Abubakar Rimi ya rasu bayan ‘yan fashi sun Kai masa farmaki a kan hanyar Bauchi zuwa Kano. Bai samu rauni ba yayin harin, sai dai daga bisani ya rasu sakamakon matsaloli masu alaka da zuciya.

Rimi dan siyasa ne da ya zama abin koyi ga ‘yan siyasa dama, har ma a na yi masa lakabi da ‘limamin canji’.

Ka’dan daga cikin ayyukan daya Gabatar yana Gwamna sun ha’da da:

1. Kai dalibai Kasashen Duniya dan karo Karatu

2. Samar da hukumar yaƙi da jahilci

3. Kafa Hukumar Ilmin Firamare

4. Hukumar Samar da Wutar Lantarki a yankunan Karkara

5. Kafa Hukumar Kula da Muhalli da Tsara Birane

6. Bai wa daliban sakandare alawus na wata-wata

7. Gina gidan Talabijin na CTV da a yanzu aka maidashi ARTV

8. Samar da gidan Jaridar Triumph

Dadai wasu ayyukan da dama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here