Babu alfarmar da Peter Obi da Kwankwaso su ke yi wa NDC- Dickson ya gargadi magoya bayansu

NDC logo 750x430

Jagoran Jam’iyyar NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya aike da gargadi mai tsauri ga magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi da abokin takararsa Rabiu Kwankwaso, inda ya gargade su da su daina rage daraja da wulakanta jam’iyyar siyasar.

Da yake jawabi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa ya musanta jita-jitar rikicin cikin gida, inda ya jaddada cewa jam’iyyar ce ke yi wa ‘yan takara alfarma da ba su dandali, bawai su ne ke yi wa jam’iyyar ba.

Da yake jawabi ga magoya bayan ‘yan takara, Dickson ya jaddada sadaukarwar da shugabannin jam’iyyar suka yi tun dadewa kafin manyan ‘yan siyasar su sauya sheka su shigo jam’iyyar.

“Peter Obi dan jam’iyya ne mai daraja a jam’iyyar mu, mu da kan mu mun sanya shi dan takarar shugaban kasa ba tare da dan adawa ba, kuma hakan yana da daraja. Babu daya daga cikinsu da ya kasance a lokacin fafutukar kafa jam’iyyar da muka yi wa rajista, ba sa nan. Ba su biya kobo daya ba, babu dan takarar shugaban kasa da ya biya ‘sisi’. Dole ne ku ba NDC daraja. Ku daina nuna kamar wani yana yi wa NDC alfarma babu wanda ya yi.

Jam’iyyar NDC da abokan aikin mu muke yi wa ‘yan takarar alfarma ta hanyar ba su dandalin mu. Ba za ka ce kana goyon bayan Peter Obi, sannan kana rage darajata a matsayin jagoran jam’iyyar kanta ba.” In ji shi.

Ya ambata wa masu suka cewa babu Peter Obi ko Kwankwaso a lokacin kafa ko rajistar jam’iyyar, inda ya ce ba su ba da gudummawar kudi ba wajen kafa ta.

“NDC ba ta sayar da tikitin takara ga mutane, “Abin da muka yi shi ne, saboda jam’iyya ta dogara ga kanta, masu neman takara su ba da gudummawa da taimako zuwa asusun jam’iyyar, inda aka rarraba zuwa matakin masu neman takara, ciki har da masu neman takarar shugaban kasa. Dan takarar shugaban kasa ya ba da gudummawa zuwa asusun yakin neman zaben shugaban kasa, ba ga wani ba, mun ba su dandalin mu ba tare da maganar kudi ba.”

Sanata ya bayyana bacin ran sa cewa magoya baya suna kokarin nuna kamar ‘yan takara ne ke yi wa NDC alfarma, yana mai cewa shugabannin jam’iyyar ne suka girmama Obi ta hanyar sanya shi dan takarar shugaban kasa shi kadai, kuma ya ce magoya bayan ba za su iya cewa suna goyon bayan dan Takara ba yayin da suke cin zarafin jagoran jam’iyyar da ya dauki nauyinsa ba.

Dangane da batutuwan zabe gaba daya, Sanata Dickson ya soki tsoma bakin Majalisar Kasa a harkokin gudanar da jam’iyyu, yana mai cewa ‘yan majalisa ba su da alaka da tilasta wa jam’iyyu yin zaben fidda gwani kai tsaye (Direct Primaries).

Ya dage cewa dole ne a bar al’amarin zabar ‘yan takara da yadda za a yi zaben fidda gwani gaba daya ga jam’iyyun yadda suke so, yana mai nuna cewa zaben fidda gwani na kai tsaye kan haifar da tarzoma inda bangarori biyu kan fitar da sakamako daban-daban da ba a da tabbaci daga mutanen da ba su da hurumi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here