Gwamnatin El-Rufa’i Ta Shirya Wa Sabbin Ma’aikata 10,000 Jarabawa

34cf884030a0fd82
34cf884030a0fd82

Hukumar ba da ilimin bai ɗaya ta jihar Kaduna, (KADSUBEB), tace ta shirya tsaf don gudanar da jarabawa ga sabbin malaman makaranta da zata ɗauka aiki.

Jaridar Daily Trust ta rawaitu cewa hukumar ta sanya ranakun 17 zuwa 28 ga watan Oktoba, 2022 a matsayi lokacin zama jarabawar a shiyyoyin jihar guda uku.

A wata sanarwa da KADSUBEB ta fitar, ta ce a shiyyar kudancin Kaduna, jarabawar zata gudana a makarantar Institute of Information Technology, Kofar Doka, Zaria.

Haka zalika a Kaduna ta tsakiya jarabawar zata gudana ne a Jami’ar jihar Kaduna (KASU) dake cikin birnin Kaduna, yayin da reshen KASU da ke Kafanchan zai wakilci shiyyar kudancin Kaduna.

A watan Yuli da ya gabata, Shugaban hukumar KADSUBEB, Malam Tijani Abdullah, ya ce gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna ya umarci hukumar ta ɗauki sabbin malamai 10,000.

Jaridar SolaceHausa ta tattaro cewa tun a zangon Mulkin Gwamna El-Rufai na farko, gwamnatin ta kori Malaman makaranta da dama bayan sun faɗi jarabawar gwaji.

Lamarin dai ya haifar da cece-kuce daga sassan jihar, inda wasu ke ganin ya kamata gwamnan ya biya Malaman hakkokinsu kafin ya sallame su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here