Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Dr. Yusuf Bello Danbatta, ya yi alkawarin yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin habbaka zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa a jihar bayan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC.
SolaceBase ta ruwaito cewa Danbatta ya yi wannan alkawari a ranar Lahadi yayin da yake bayyana godiyarsa ga shugabannin APC, ‘yan jam’iyya, magoya baya da al’ummar Karamar Hukumar Danbatta bisa yadda suka tarbe shi yayin yin rajistar zama cikakken memba na jam’iyyar mai mulki.
Ya ce yawan jama’ar da suka nuna goyon baya da hadin kai ya kara karfafa masa azama wajen bayar da gudunmawa ga manufofin jam’iyyar da ci gaban Jihar Kano.
“Yawan jama’ar da suka fito, hadin kai da karfafa gwiwar da aka nuna a wannan taro ya kara karfafa azamanata don ci gaba da aiki tare da duk masu ruwa da tsaki wajen habbaka zaman lafiya, ci gaba da bunkasa jihar mu mai daraja,” in ji shi.
Ya ce ya na jin nauyi da kwarin gwiwa da kyakkyawar niyyar da aka nuna masa, inda ya sake tabbatar da kudurin sa na habbaka manufofin APC da tallafawa manufofin da za su kawo hadin kai da ci gaba mai dorewa a fadin jihar.
Danbatta ya bayyana godiya ta musamman ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Shugaban APC na Jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa da mambobin Kwamitin Zartarwa na Jihar na jam’iyyar bisa goyon bayansu da karfafa masa gwiwa.
Haka kuma ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Danbatta, Jamilu Abubakar, bisa karbar bakuncin taron da kuma jagoranci da bakin da ya bayar wanda ya taimaka wajen samun nasarar taron.
Tsohon kwamishinan ya kuma yaba wa wakilin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wakilin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo, Kwamishinan Kudi da na Ayyuka da sauran shugabannin jam’iyya, masu rike da mukamai, mambobin Kwamitin Gudanar da Taron a gida, abokai da magoya baya bisa halartar taron.
Ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba da zaman lafiya, hadin kai da wadata ga Jihar Kano da Najeriya baki daya.













































