Matar da ta tinjima tafkin Legas ma’aikaciyar DSS ce

Adetutu Adedokun
Adetutu Adedokun

Rahotonni sun ce matar da ta tsindima tafkin ruwa a ikko rijiya ranar Alhamis da yamma an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, kuma ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya ce DSS.

Majiyoyi a ofishin hukumar sun bayyana cewa jami’a ce cikin hukumar dake koyar da dabarun yaki ba da makami ba.

Kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta rawaito a ‘yan watannin da suka gabata, Adedokun wacce ta cika shekara 30 da haihuwa, ta samu takaddar yabo daga Darakta Janar na DSS a matsayin wadda ta fi kowa yin yaki a cikin sa.

An kuma bayar da rahoton cewa saurayin wanda aka kashe ya nemi aurenta makonnin da suka gabata. Yayin da ta sauka daga motar haya ta Uber a kan gada kuma ta fada cikin tafkin kogin ranar Alhamis da yamma. Direban tasi ya yi ikirarin cewa tana ta musayar zazzafan kalamai da saurayin nanta kafin ta sauka daga motar.

Jim kadan bayan faruwar lamarin, sai ga jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas da jami’an hukumar DSS, suka dauki matakin nemo wadda abin ya shafa.

Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, a wata sabuwar sanarwar da ya fitar ya ce har yanzu tawagar masu aikin ceto na kan ruwa suna ta kokari dan gano gawar ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here