Sojojin saman Najeriya sun biya diyya ga waɗanda harin soji a Sokoto ya shafa

IMG 20251221 WA0048 750x430

Rundunar sojojin saman Najeriya ta biya diyya ga mutanen da harin sojin sama bisa kuskure abin ya shafa da kuma iyalan waɗanda suka rasu a jihar Sokoto.

Harin ya shafi al’ummomin unguwannin Gidan Bisa da Rumtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame, inda aka samu asarar rayuka da jikkata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a da yada bayanai na rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja

Sanarwar rundunar ta nuna cewa an dauki matakin biyan diyya ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tausaya wa jama’a da kuma gyara abin da ya faru.

Rundunar ta bayyana cewa tana daraja dangantakarta da al’ummomi tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula.

Babban hafsan sojojin saman Najeriya ya yaba da rawar da gwamnatin jihar Sokoto ke takawa wajen ƙarfafa tsaro da haɗin kan jama’a, musamman ta hanyar manufofin tsaro da aka samar a matakin jiha.

Ya nuna cewa irin waɗannan matakai na cikin gida suna taimakawa ayyukan tsaro na tarayya wajen rage ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.

Idan za a iya tunawa, harin saman ya gudana ne a ƙarƙashin wani aikin soja bayan samun bayanan sirri da ke nuna motsin wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin.

Duk da bin matakan tantance bayanai kafin kai harin, daga bisani bincike ya tabbatar da cewa fararen hula 13 sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas suka jikkata.

Rundunar ta bayyana cewa sakamakon binciken ya jefa ta cikin jimami tare da sa a ɗauki matakan gaggawa na diyya domin rage raɗaɗin da jama’a suka fuskanta.

Gwamnan jihar Sokoto ya nuna godiya ga rundunar sojojin saman Najeriya bisa jajircewarta wajen kare jama’a da tabbatar da tsaron ƙasa, tare da bayyana cewa biyan diyya ya nuna ɗaukar alhaki da girmama rayuwar fararen hula.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here