Kamfanin FRIDABS Solacebase Communications Limited, masu wallafa jaridar Solacebase ta internet, ya shirya liyafar cin abinci a Kano jim kaɗan bayan kammala bitar ayyukan ofishin na ƙarshen shekara, inda manyan mutane daga bangarorin shari’a da aikin jarida suka hallara tare da yabawa ƙungiyar kan ƙwarewa, sahihanci da kuma ƙaruwar tasirinta a fagen aikin jarida a Najeriya.
A yayin taron, shugaban ƙungiyar lauyoyi ta kasa a nan Kano NBA reshen Ungoggo, Ahmed Abubakar Gwadabe, ya bayyana Solacebase a matsayin amintacciyar abokiyar hulɗa ga ƙungiyoyi daban-daban ciki har da ƙungiyar lauyoyi da masu aikin shari’a, inda ya nuna rawar da take takawa wajen tallafa musu da yaɗa ayyukansu.
Ya kuma bayyana cewa labaran da Solacebase ke wallafawa suna samun karɓuwa sosai a cikin jama’a, tare da bin ƙa’idojin aikin jarida na duniya, musamman a rahotannin da suka shafi rayuwar al’umma, wanda hakan ke ƙara yawan masu karantawa daga ciki da wajen ƙasa.
Sakataren ƙungiyar ’yan jarida reshen Kano NUJ, Salim Umar Ibrahim, ya bayyana Solacebase a matsayin ɗaya daga cikin manyan jaridun Internet a jihar Kano da Arewa gaba ɗaya, yana mai cewa tsawon shekaru tana kasancewa amintacciyar tushen bayanai.
Labari mai alaƙa: Jaridar SolaceBase ta ƙuduri aniyar ci gaba da gudanar da aikin jarida bisa ƙa’ida
Ya kuma yaba da ci gaban da ƙungiyar ta samu daga kafar Internet mai sauƙi zuwa cikakkiyar kafar watsa labarai ta zamani da ke samar da shirye-shirye na bidiyo da sauti, tare da ba da horo da aikin yi ga matasa cikin bin ƙa’idojin ɗabi’a da ƙwarewa.
Tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Kano, Abdurrazak Aikawa, ya bayyana Solacebase a matsayin ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labarai mafi sahihanci a wannan zamani da ake fama da yaɗuwar labaran ƙarya, yana mai cewa duk wani labari da ya fito daga Solacebase ana ɗaukarsa abin gaskiya ne kuma an tantance shi.
Taron bitar ƙarshen shekara da liyafar karɓar baki sun nuna ƙudirin Solacebase na ƙara ƙarfafa aikin jarida mai ɗabi’a, faɗaɗa ayyukanta a kafafen zamani da kuma zurfafa amincewar jama’a yayin da take shirin fuskantar ƙalubale da damar da sabuwar shekara za ta zo da su.












































