Gwamnatin jihar Borno ta sanar a ranar Litinin cewa Naira biliyan 4.4 ne kacal daga cikin Naira biliyan 13.1 da aka bayar don tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa a Maiduguri.
Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ne ya bayyana hakan a Maiduguri.
Tar ya bayyana cewa, an mika kudaden ne ga kwamitin rabon tallafin da masifu da aka kafa a baya-bayan nan, wanda ya kunshi wakilai daga hukumomin tarayya da na jiha, da masu fasaha, shugabannin gargajiya da na addini, da hukumomin tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, NSCDC, DSS, EFCC. da ICPC.
Kwamitin dai yana da alhakin tabbatar da yadda aka biya kudaden ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Tun da farko Gwamna Babagana Zulum ya kaddamar da shirin tallafin kudi na zagayen farko ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa domin fara sake gina gidajensu.
Tar ya ba da tabbacin cewa wadanda abin ya shafa da suka riga sun sami abinci da tsabar kudi har zuwa makonni biyu za su sami ƙarin taimako.
Kwamishinan ya yi magana kan ikirarin cewa an tilasta wa wasu da abin ya rutsa da su barin sansanonin, yana mai bayyana cewa yayin da da dama suka koma gida yayin da ruwa ya ja, babu wanda ya tilasta wa barin.
Gwamnati na shirin hada wasu sansanoni musamman wadanda ke cikin makarantu domin baiwa dalibai damar ci gaba da karatunsu.
Tar ya kuma kara da cewa ana ci gaba da kokarin tallafawa wadanda abin ya shafa da suka zabi zama a wajen sansanonin, barci a kan tituna, wuraren kasuwanci, da sauran wurare.
Gwamnati ta fara rajista da bayar da tallafi ga wadannan mutane, tare da karfafa musu gwiwa su koma sansanonin.