An kawar da wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Kachalla Sani Black.
‘Yan bangan da suka “gama” dan ta’addan sun kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, da tsabar kudi da ba a bayyana adadinsu ba da kuma bindigar PKT.
PRNigeria ta kara da cewa ‘yan banga na yankin sun kashe Kachalla da ‘ya’yansa biyu a wani harin kwantan bauna da suka kai a Magama Mai Rake, a karamar hukumar Maru.
Kachalla Sani Black, babban dan tawagar da Bello Turji a harkar ‘yan fashi, ya kasance fitaccen shugaban ‘yan fashi da ke aiki a Chabi, yankin Dan Sadau a karamar hukumar Maru.
PRNigeria ta rahoto cewa Sani-Black wani dan bindiga ne da ya shahara wajen ta’addancin al’umma da matafiya a Arewacin Zamfara, yaran sa sun kai hare-hare a jihohin Kaduna, Neja da Kebbi. A lokacin, babu wani shugaban ‘yan fashi da ya goyi bayan tasirin Kachalla Sani Black a Dan Sadau.