Medview yayi bayani akan kashe kudaden aikin Hajji, yayin da EFCC ke binciken kamfanin jirgin

E4AA6D4B F63F 4C99 980D E8B106C6036F
E4AA6D4B F63F 4C99 980D E8B106C6036F

Kamfanin na Medview Airline Plc ya fayyace cewa an yi amfani da kudin da aka ware na aikin Hajjin 2019 don shirye-shiryen da suka dace da suka hada da kula da jirage da kuma biyan masu ba da sabis.

Babban Daraktan Kamfanin na Harkokin Kasuwanci, Mista Isiaq Na-Allah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Legas ranar Juma’a.

Na-Allah ya musanta cewa kamfanin jirgin  yana da hannu wajen zamba ko karkatar da kudaden da aka tanada don jigilar Hajjin 2019.

Ya ce an ja hankalin kamfanin a kan rahotannin da kafafen yada labarai suka rika yadawa kan badakalar da aka yi biyo bayan gayyatar da shugaban hukumar, Alhaji Muneer Bankole, da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta yi masa.

Na-Allah ya ce gayyatar an gayyace shi ne domin yin karin haske kan kwangilar aikin Hajji da kamfanin jirgin ya yi da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).

Ya ce: “Musamman daga cikin dala 900,000 da aka kashe, NAHCON ta biya kudaden ne kai tsaye ga wasu kamfanoni guda biyu da ke Saudiyya, wato General Authority of Aviation ($ 400,000 da Taibah Developments Development Company ($500,000), a ranar 5 ga Yuli, 2019.

“Duk da yunkurin da wasu manyan mutane ke yi na dakile ayyukan kamfanin tare da sakin kudade, kamfanin Medview Airline ya yi jigilar maniyyata 4,387 daga jihohin Kaduna, Yobe da Ogun. Hukumomin Alhazai na wadancan jahohin dai su ne shaidun da suka tabbatar da aikin.”

“A bisa ka’idar kwangilar da NAHCON ta yi, an kafa babban kwamiti don daidaita bambance-bambancen da ake samu na biyan kudin jirgin da kuma adadin maniyyatan da aka yi jigilar su ta jirgin, inda aka warware dukkan matsalolin.”

Don haka Na-Allah ya ce “abin mamaki ne wani ya farka daga bacci ya hau rufin gida, ya busa kaho da kuge da yin zambar cewa an karkatar da kudade. Duk wanda  ya yi haka to ya yi wa  kamfanin Medview Airline Plc sharri”.

Ya yi nuni da cewa, kamfanin jirgin ya jajirce wajen komawa kan aikinsa na jagoranci a ayyukan Hajji.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa a ranar 2 ga watan Fabrairu ne hukumar EFCC ta yiwa Manajan Daraktan kamfanin na Medview Airline, Muneer Bankole tambayoyi bisa zargin zamba.

An tsare Bankole ne a hedikwatar EFCC da ke Abuja, bayan gayyatar da masu bincike suka yi masa.

Lamarin dai na da nasaba da karkatar da kudaden, inda ake zargin Bankole da rike kashi 50 na kudaden da NAHCON ta biya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here