Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince wa jami’an tsaro su shiga rumbun adana bayanai na hukumar tantance ‘yan Najeriya a yayin gudanar da ayyukansu.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Isa Pantami, ya ce ofishinsa ta hannun Hukumar Sadarwa ta Najeriya, ya mika takardar amincewa ga hukumomin tsaro da abin ya shafa.
Ko da yake Pantami bai bayyana sunayen hukumomin tsaro ba. Sai dai ya ce ci gaban zai inganta tsaro domin zai taimaka wa jami’an tsaro wajen ganin bayan masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jaridun Najeriya a gefen taron fasaha na LEAP 22 da ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a halin yanzu.
Pantami ya ce, “Wasu daga cikin hukumomin tsaro, bisa ka’idar aikata laifuka ta yanar gizo, an ba su damar shiga rumbun adana bayanai ba tare da sun zo wurinmu ba, saboda rumbun adana bayanan na ba da damar shiga cikin doka.
A shekarar 2020 ne gwamnatin tarayya ta ba da umarnin haɗa lambar ‘yan kasa NIN da layikan waya wato SIM ga kowane mai amfani da wayar.
Ya bayyana cewa an ba da damar irin wannan dama ne domin a tallafa wa jami’an tsaro.
“Malam Shugaban kasa ya ba su izini su yi shi, ba tare da mu ma mu sa baki ba. Don haka, da wannan amincewar, NCC ta isar da hakan ta ofishina ga dukkan hukumomin da abin ya shafa cewa Shugaban kasa ya amince da hakan,” in ji Ministan.
Ya kara da cewa gwamnati na kokawa wajen biyan albashi da kuma aiwatar da matakan da za su taimaka wa hukumar ta kammala aikin ta.













































