Babbar KotunJihar Kano a ranar Alhamis ta yanke wa wata mata mai shekaru 19, Saudat Jibrin, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe mijinta mai shekaru 30, Salisu Idris, kwanaki 9 bayan daura aurensu.
An tuhumi Saudat, wadda ke zaune a Karamar Hukumar Kumbosto ta Kano, da laifin kisan kai.
Da take gabatar da hukuncin, Mai Shari’a Maryam Sabo, ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.
“Na yanke wa Saudat Jibrin hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan kai. Kina da kwanaki 90 don daukaka kara,” in ji alkaliyar.
Tun da fari, Lauya Mai Gabatar da Kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa Saudat Jibrin ta aikata laifin a ranar 5 ga Mayu 2025, a unguwar Farawa dake Kano.
Ya ce da misalin karfe 9 na dare, Saudat ta zuba guba a abin shan mijinta sannan ta yanka makogwaronsa da wuka kwanaki 9 bayan aurensu.
Abba-Sorondinki ya gabatar da shaidu 2 domin tabbatar da kara a kan wanda ake tuhuma.
Wadda ake tuhuma ta musanta aikata laifin.
Lauyan ya ce laifin ya saba wa tanadin Sashi na 221(a) na Dokar Laifuka ta Penal Code.
Lauyan karewa, Abdulfatah Muhammad, ya gabatar da wanda ake tuhuma don ta kare kanta. Muhammad ya roki kotu ta yi la’akari da cewa, ta sauya halinta a lokacin da ake tsare da ita a gidan gyaran hali, inda ta haddace Alkur’ani Mai Tsarki.
Haka kuma ya roki kotu ta yi la’akari da cewa ita ce babbar ‘yar a wurin iyayenta kuma ‘yan uwanta sun dogaro da ita wajen rayuwa.
NAN













































