Rahoto na Musamman: Nihal da matsalolin dukan yara a makarantu

IMG 20260629 WA0024

Mutuwar wata dalibar karamar sakandare, Maimuna Sani Salisu mai shekaru 13, wadda aka fi sani da Nihal, ta girgiza jama’a a jihar Kano da kasa baki daya.

Duk da cewa ana ci gaba da bincike kan yadda ta rasu, martanin jama’a kan wannan mummunar lamarin ya bayyana wani abu mai zurfi fiye da neman amsa kan shari’ar guda daya kawai.

A karshen makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin bincike kan mutuwar Maimuna, dalibar St. Louis College wadda ake zargin ta rasu ne sakamakon duka ta horo.

Yadda mutane suka fusata sosai ya nuna damuwa da ke karuwa kan yadda ake mu’amalantar yara a makarantu da kuma ci gaba da dogaro da dukan yara a matsayin horo, duk da gargadin da ake yi akai-akai kan hadarin hakan.

Ko binciken zai iya tabbatar wa ko ya karyata zargin cewa duka ne ya haddasa rasuwar Nihal, tambayoyin da wannan lamari ya tayar ba za a takaita su ga makaranta guda, malami ko dalibai guda daya ba.

Sun shafi wata babbar matsala da ta dauki tsawon shekaru a cikin tsarin ilimi da koyarwa a Najeriya. Batun Nihal ya zama abin da ya ja hankali ba don tana da banbanci ba, sai dai don ta tuna wa ‘yan Najeriya da irin abubuwan da suka faru a baya.

Nuna damuwar na da dalili, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ana kiyasta cewa kimanin yara biliyan 1 da miliyan dari 2 a duk duniya suna fuskantar dukan a kowace shekara.

Hukumar ta na yin gargadi akai-akai cewa dukan yana cutar da lafiyar jiki da hankalin yara, yana kuma kara matsalolin halayya kuma ba ya da wani sakamako mai kyau ga ci gaban su.

A Najeriya, sakamakon binciken 2021 na Multiple Indicator Cluster Survey ya nuna cewa yara tara cikin goma masu shekaru 1 zuwa 14 sun fuskanci wani nau’in horo mai tsanani.

Haka ma UNICEF ta bayar da rahoton cewa kusan kashi 85 na yaran Najeriya suna fuskantar horo mai tsanani a makarantu, yayin da kusan kashi daya cikin uku ke fuskantar mummunan duka a jiki.

Wadannan alkaluma na nuni da cewa matsalar ba ta takaita ga makarantu kadai ba, ta zama al’ada da ta yadu wadda har yanzu tana danganta horo da zafi.

Ga mazauna Kano, labarin mummunan lamarin da ya faru a shekarar 2025 a makarantar gwamnati ta kwana da ke Bichi har yanzu yana nan a zuciyarsu.

An ruwaito dalibai biyu sun mutu bayan wani horo da abokan karatunsu suka yi musu, wanda ya haifar da kama mutane da kuma sake haifar da damuwa kan al’adar duka a makarantu.

Wannan ya faru kusan shekara guda kafin labarin Nihal, lamarin Bichi ya nuna cewa damuwa kan tsaron dalibai a makarantun ilimi ba sabo ba ne, kuma ba shi da nisa.

Lamarin bai takaita ga Kano kadai ba, a shekarar 2018, mutuwar Rayyan Ahmad, dalibin aji 2 a Babbar Sakandiren Gwamnati ta jeka ka dawo ta Sankalawa a Jihar Zamfara, ya haifar da tattaunawa a fadin kasar bayan rahotanni sun danganta mutuwar sa da dukan da malami ya yi masa.

Ko da yake ‘yan uwan sa daga baya sun musanta cewa dukan ne ya haifar da mutuwar, lamarin ya bayyana hadarin da ke tattare da dukan yara a matsayin horo.

A shekarar 2021, rikici ya barke a fadin kasa bayan wani bidiyo ya bazu da ke nuna daliban wata makarantar Allo a Ganm a jihar Kwara, inda malamansu suke dukan su da dogayen sanduna.

Martanin ya yi tsanani har gwamnatin jihar ta kafa kwamiti wanda alkalin mai ritaya ya jagoranta don bincika lamarin da ba da shawarar yadda za a hana sake faruwar sa.

Shekarar da ta biyo ma ta 2022, Hauwa’u Salihu, dalibar Makarantar Gidauniyar Rochas da ke Zaria a Jihar Kaduna, ta samu mummunan rauni a wuya kuma ta tsira da wuya daga lalacewar kashin baya bayan an zargi malami da buge ta a yayin hukunci.

Wata damuwar mai kama da irin wannan ta faru a baya a shekarar 2017 lokacin da Raliya Suleiman, dalibar Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kachai, ta rasa gani a idonta na dama bayan sandar malami ta buge ta yayin horo kan rashin zuwa makaranta a kan lokaci.

A dai wannan shekarar, wani lamarin ya sake yawo hankalin jama’a, inda Nuhu Yahya na Kwalejin Gwamnati ta Tarayya, Kwali, wanda ake cewa ya mutu bayan malami ya buge shi.

Wadannan abubuwan sun kara tabbatar da damuwar cewa horon da aka yi da niyyar gyara halayya, a wani lokaci kan iya haifar da sakamako mai illa ga rayuwa.

Damuwar ba ta takaita ga Arewa ba, a watan Oktoba 2024, an ruwaito wani dalibi mai suna Monday Arijo ya mutu bayan malaminsa ya yi masa horon duka.

A watan Janairu 2025, al-ummar kasa sun nuna bacin ransu, bayanbullar wani bidiyo da ke nuna malami na marin wata yarinya ‘yar shekara uku a wani aji a Legas.

Abin da ya sa lamarin ya fi daukar hankali shi ne cewa iyaye da malamai da yawa sun amince cewa irin wannan hali ba sabon abu ba ne.

Ya zama babban abin tattaunawa a tsakanin ‘yan kasa saboda an dauke shi da kyamara.

Idan aka yi dub ana tsanaki, za a ga kowanni lamari na daban ne, zai iya zama kamar ba na yau da kullum ba ne. Amma idan aka hada su baki daya, suna nuni da wata matsala da ke ci gaba da maimaituwa.

Sunaye, wurin da abin ya faru da yanayin sa sun bambanta, amma ma’anar da ke kunshe guda daya ce. Akai-akai, ana fitar da zarge-zargen duka da ya wuce haddi, wanda ke haifar da damuwa kan dangantakar da ke tsakanin horo da azabtarwa.

Ci gaba da faruwar wadannan abubuwa na nuna cewa matsalar ba ta’allaka ga malami guda ba. Ta samo asali ne a cikin akidar da ta dade ta cewa tsoro wani kayan aiki ne mai tasiri a ilimi kuma jikin mutum ya fada masa halattacciyar hanya ce don horo.

Sai dai shekaru da dama na bincike sun nuna akasin haka. Yaran da ake duka da tashin hankali suna iya fuskantar damuwa, bacin rai, fushi, sakamakon karatu mara kyau da damuwa a hankali na dogon lokaci.

Shaidu suna kara nuna cewa dukan yara na iya samun biyayya nan take, amma sau da yawa a farashin lafiyar yaron.

Tattaunawar da ‘yan Najeriya ke ci gaba da yi kan dukan yara idan aka kwatanta da abin da ke faruwa a wasu kasashe da suka cigaba.

A cikin shekaru da suka gabata, kasashe irin su Sweden, Finland, Norway, Jamus, Afirka ta Kudu da New Zealand sun haramta dukan yara a makarantu ko a duk wani wuri da ya shafi yara.

Kwarewar su ta nuna cewa ana iya yin horo ba tare da amfani da tashin hankali ba kuma cewa iko a makaranta bai dogara da bulala ba.

Najeriya ba ta rasa dokoki da manufofi da aka tsara don kare yara ba, dokar kare hakkokin yara da yarjejeniyoyin kasa da kasa da kasar ta rattaba hannu a kai suna jaddada kare yara daga tashin hankali, azabtarwa da mu’amala mai wulakantawa.

Kalubalen shi ne yadda za a mayar da wadannan ka’idoji zuwa aiki na zarihi na yau da kullum a makarantu, rahotannin da ke ci gaba da fitowa na dukan da ya wuce haddi na nuni da wani gibi na damuwa tsakanin manufofi da abin da ke faruwa a zahiri.

Ana yawan gabatar da wannan tattaunawa kamar zabi ne tsakanin horo da rashin horo. Amma ba haka ba ne, makarantu suna bukatar horo, tsari da lissafi.

Sai dai horo ba yana nufin zalunci. Ana iya gyara yaro ba tare da wulakanta shi ba. Ana iya shiryar da dalibi ba tare da raunata shi ba.

Tambayar gaskiya ba ita ce ko makarantu za su horar da yara ba, sai dai ko ya kamata dukan jiki ya ci gaba da kasancewa a cikin wannan tsari.

Saboda da haka, darasin lamarin Nihal ya wuce binciken da ke gudana, tunatarwa ce cewa duk wani zargi na duka da ya wuce haddi ya cancanci a bincike shi da muhimmanci.

Tunatarwa ce cewa manufofi ba su da amfani idan ba a aiwatar da su ba. Tunatarwa ce cewa malamai suna bukatar horo kan hanyoyin horarwa da ba su hada da duka ba kuma wajibi ne makarantu su kafa tsarin kare dalibai mai inganci.

Mafi muhimmanci, tunatarwa ce cewa al’umma dole ta daina kallon kowane sabon lamari a matsayin mummunan abu da baa so a sani. Sunaye na iya canzawa. Wurare na iya bambanta. Bayanai na iya sabawa. Sai dai matsalar da ke kunshe tana nan iri daya.

Yayin da mazauna Kano ke jiran sakamakon bincike kan mutuwar Nihal, tsammani zai kasance ya mai da hankali kawai kan yanayin yadda wannan yarinya daya ta rasu. Wannan zai zama kuskure.

Babbar matsalar da ke fuskantar kasa ita ce ko zata shirya fuskantar al’adar da ke ci gaba da haifar da tashin hankali da sunan razani ko horo.

Baza a iya auna gaskiyar irin damuwa da fushin da ake bayyanawa yau ba, sai dai gyare-gyaren da za a yi gobe.

Al’umma da ta mika amanar ‘ya’yanta ga makarantu ba za ta iya yin shiru ba idan makarantun da suka kamata su zama wurin koyo suka zama wurin tsoro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here