‘Yan Najeriya 98,000 za su samu bashin lamuni na gwamnatin tarayya

Hajiya Sadiya Umar Farouq
Hajiya Sadiya Umar Farouq

Gwamnatin Tarayya ta ce ta kammala shirin bayar da bashin lamuni marar riba ga ma’aikatanta 98,000 da suka ci gajiyar shirinta na kasuwanci da karfafawa gwamnati, GEEP, 2.0 a fadin kasar nan.

Sadiya Umar-Farouq, ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da Nneka Anibeze, mai taimaka mata ta musamman kan harkokin yada labarai ta fitar a Abuja ranar Laraba.

Mrs Umar-Farouq ta ce an cimma wannan matsayar ne biyo bayan tantance masu neman shiga mataki na 1, wadanda suka cancanta kuma aka zabo su don cin gajiyar kananan lamuni daga N50,000 zuwa N300,000.

Ta ci gaba da cewa duk wadanda suka ci gajiyar shirin na GEEP 2.0 za su samu sakon taya murna da wayar da kan su a cikin kwanaki masu zuwa na sanar da su cancantar su.

A cewar Umar-Farouq, kudaden da ake bai wa wadanda suka ci gajiyar shirin tallafin aro ne ba tallafi ba kuma dole ne a biya su cikin watanni tara.

Ministar ta ce an ba wa wadannan manoma rancen kudi naira 300,000 domin amfanin gonakin, inda ta kara da cewa shirin yana da watanni 12.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here