Gwamnonin jihohi 36 sun jaddada aniyarsu ta hada gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen daidaita haraji da cire shingayen binciken ababen hawa tare da inganta zirga-zirgar kayayyaki a fadin Jihohi.
Gwamnonin sun yi wannan alkawarin ne bayan taron kungiyar gwamnonin Najeriya NGF a Abuja, a wata sanarwar da shugaban kungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya sanya wa hannu, kuma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya karanta inda ya sanar da hakan.
Sanwo-Olu ya bayyana cewa, taron da aka gudanar ya tattauna ne kan batutuwan da suka shafi kasa musamman ma matsalar tsadar kayan abinci a fadin Najeriya.
“Yayin taron gwamnonin sun saurari bayani daga mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu wanda ke tare da rakiyar ministocin tsaro da na noma da raya dabbobi da na Sufuri, kan tashin farashin abinci da sufurin dabbobi a fadin kasa Najeriya.
Sanwo-Olu wanda ya ce, taron ya kuma samu gabatarwa daga bankin duniya kan shirin NG-CARES, ya bayyana damuwar gwamnonin kan rashin cika alkawuran da bankin ya yi na samar da kudade a karkashin shirin NG-CARES 1.0.
Ya kara da cewa, “Bankin ya bayyana cewa, jihohin sun zuba jarin da suka kai sama da dalar Amurka biliyan 2.2 ta hanyoyin samar da kayayyaki na NG-CARES, tare da tabbatar da tasirin da ya kai sama da mutane miliyan 17 da suka amfana kai tsaye.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa taron wanda aka kammala shi da sanyin safiyar yau Alhamis, ya samu halartar gwamnonin Kwara da Oyo da Imo da Anambra sai Akwa-Ibom da Osun da Filato.
Sauran sun hada da gwamnonin Lagos da Nasarawa da Ekiti da Ebonyi da Kogi da Ondo sai Cross-River da Ogun da Edo.
NAN













































