Dubban magoya baya sun tarbi gwamna Abba Kabir daga aikin Hajji

WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.10 1 768x432

A yau Laraba ne dubban al’ummar Kano suka tarbi gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, a lokacin da ya dawo daga aikin Hajjin bana.

Jirgin da ya kawo gwamnan da tawagarsa daga kasar Saudiyya ya tsaya ne a Lagos inda daga nan kuma suka sauka a Kano da misalin ƙarfe 2:50 na rana.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa ɗimbin jama’ar da suka raka gwamnan daga filin jirgin sama a tafiyar kasa da mintuna ashirin zuwa gidan gwamnati ta hanyar Murtala Mohammed sun kwashe sama da sa’o’i biyar.

An gano gwamna Abba Yusuf ya na daga hannu ga mazauna garin cikin yanayi na jin daɗi.

Da ya ke zantawa da manema labarai a kan dawowar gwamnan, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana irin farin cikinsa bisa ganin ɗimbin jama’ar da suka tarbi gwamnan.

“Daga cikin jama’ar da suka tarbi mai girma Gwamna yau a filin jirgin sama da kuma hanyarsa ta zuwa fadar gwamnatin Kano, shaida ce da ke tabbatar da cewa, ƴan jihar Kano sun gamsu da yadda mai girma gwamna ya samar da sauyi da ci gaba musamman a fannin ababen more rayuwa.

“Abubuwan da mai girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar yi sun haɗa da farfado da cibiyoyi 26 da gwamnatin da ta shude ta yi watsi da su, da ci gaba da shirin bayar da tallafin karatu na Kwankwasiyya na gida da waje, da inganta manyan asibitoci guda 11, biyan kudin jarrabawar kammala Sakandare SSCE ga dalibai 141,175 da bunƙasa manufofin sauyin yanayi na jihar Kano sai gina masana’antar samar da wutar lantarki da dai sauransu.

WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.13 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.04 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.10 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.07 1 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.00 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 18.55.28 768x432 WhatsApp Image 2025 06 18 at 19.44.10 1 768x432

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here