Kungiyar Alkalai ta Kasa (MAN) reshen Jihar Kwara, ta sanar da shirinta na shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Alhamis 2 ga Yuli 2026, kan karancin biyan albashi, rashin biyan alawus-alawus da kuma wariyar da ake nuna wa alkalan jihar a fannin jin dadinsu.
An sanar da wannan shawara ne a cikin wata takardar bayan taro da aka fitar bayan wani zaman gaggawa na alkalan da aka gudanar a ranar Laraba, inda mambobi suka bayyana takaici kan abin da suka kira da shakulatun bangaro da gwamnatin jihar ta yi da su tsawon shekaru.
A cewar sanarwar da Shugaban (MAN) na Jihar Kwara ya sanya wa hannu, alkalan sun bukaci a dauki mataki nan take kan wasu batutuwa na jin dadinsu, ciki har da sake duba albashi, biyan alawus-alawus da suka rage da kuma rabon motocin aiki daidai.
Kungiyar ta koka kan cewa Alkalin da ke mataki na 14 a yanzu yana samun kasa da albashin da rijistaran kotu mai mataki na 14, inda ta bayyana lamarin a matsayin rashin adalci da ya rage kimar jami’an shari’a.
Alkalan sun kuma koka kan rashin biyan alawus din kayan ofis, wanda ake sa ran biyan shi duk bayan shekaru 4.
A cewar kungiyar, an biya wannan alawus din a karon karshe ne a mulkin tsohon Gwamna Abdulfatah Ahmed.
Sauran korafe-korafen da alkalan suka gabatar sun hada da rashin biyan wasu alawus-alawus da kuma zargin wariya wajen rabon motocin aiki, inda wasu alkalan aka ba su motoci yayin da wasu aka watsar da su gaba daya.
Sanarwar ta bayyana cewa mambobi kungiyar da fari sun bukaci yajin aikin ya fara cikin sa’o’I 48 saboda tsananin bacin ran da suke ciki, sai dai alkalin alkalai na Jihar ya ba da shawara cewa duk wata sanarwa ta wa’adi dole ta bi tsari kuma kada ta kasance kasa da kwanaki 7.
Bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin alkalan da hukumomin shari’a, bangarorin biyu sun amince a ba da wa’adin kwanaki 7, wanda ya hada da kwanakin karshen mako.
Kungiyar ta roki mambobin ta da su kwantar da hankali, su kasance cikin hadin kai, inda ta tabbatar musu cewa ana cigaba da kokari don samun sakamako mai kyau.













































