Lalata kayayyakin wutar lantarki ya jefa al’ummomin Kano cikin duhu tsawon shekaru

IMG 20260624 WA0017 750x430

Sata da lalata kebulan wutar lantarki da kayan aikin na ci gaba da sa al’ummomi da dama a kananan hukumomin Minjibir, Makoda da Dambatta a Jihar Kano cikin rashin wutar lantarki sama da shekaru 10.

Darakta Janar na Sashen Bincike da Takardu (RDD) na Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Nana Asma’u Jibrin ce ta bayyana haka yayin ziyar tantance barnar da aka yi wa kayan wutar lantarki da aka yi a yankunan da lamarin ya shafa.

Jibrin, wadda Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga na sashen, Malam Bello Garba ya wakilta, ya ce wannan aiki na da nufin gano dalilan da ke sa ake ci gaba da lalata kayan aiki da kuma tantance tasirin da yake yi wa mazauna yankin.

Tantancewar, kamar yadda ya ce, ta shafi manyan hanyoyin layin wuta da ke hada garin Minjibir da Kunya, Kwanar Dumawa da Kore da kuma garuruwan Wailari da kewaye da sauransu.

Ya ce yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, wakilan za su tattara bayanan gaskiya kan girman barnar da kuma yadda ta shafi harkokin zamantakewa da tattalin arzikin al’ummomin da abin ya shafa.

Darakta ya bayyana kyakkyawan fata cewa shawarwarin da za su fito daga tantancewar za su taimaka wa gwamnati wajen dakile lalata kayayyakin jama’a da kuma tabbatar da samar da wutar lantarki mai dorewa a yankunan da abin ya shafa.

Shugaban Karamar Hukumar Makoda, Alhaji Lawan Jibga, ya koka da cewa satar da ake yi na kebul da lalata kayan aikin wuta ya hana al’ummomi da dama samun wutar lantarki tsawon shekaru.

A cewarsa, lamarin ya tilasta majalisa ta nemi wasu hanyoyin samar da wuta ga mazauna yankin.

Jibga ya kara da cewa majalisa ta shigar da na’urorin da ke amfani da hasken rana a wasu daga cikin yankunan da abin ya fi shafa domin inganta samun wutar lantarki da tallafawa harkokin kasuwanci.

Ya bukaci gwamnati ta shiga cikin lamarin domin dawo da wutar lantarki da kuma daukar matakan kare kayayyakin jama’a daga ci gaba da lalacewa a yankunan. NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here