Abuja Zuwa Kaduna: Hukumar NRC ta bayyana dalilin lalacewar wani jirgin kasa

Jirgin, Kasa, NRC, Abuja, Kaduna, Hukumar, bayyana, dalilin, lalacewar, wani
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta bayyana cewa matsalar fasaha da aka samu a kan hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta bayyana cewa matsalar fasaha da aka samu a kan hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda ya kai ga karkatar da layin dogo a yammacin Larabar da ta gabata, ya faru ne sakamakon cire faifan na’urar nadar titin da barayi suka yi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama’a, Yakub Mahmood, a ranar Alhamis.

Karin labari: Hajjin Bana: Hukumar NDLEA ta kama alhazai da ke ta’ammali da kwayoyi

Sanarwar ta bayyana cewa barayin sun cire faifan na’urar da ke lankwasa titin wanda ya kai ga karkatar da layin a tashar jirgin kasa ta Asham da ke jihar Kaduna.

“An danganta wannan ƙaramar matsala da cire faifan bidiyo na lallasa waƙa da ɓangarori suka yi. Koyaya, Gudanar da NRC ya ci gaba da tsayawa tsayin daka don tabbatar da amincin fasinjojinmu masu kima a cikin tsarin gaba ɗaya, “in ji shi.

Idan dai za a iya tunawa dai wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kauce hanya a tashar Asha, lamarin da ya sa fasinjoji da dama suka makale a babban birnin tarayyar Abuja.

Karin labari: Majalisar dokoki a Kaduna ta ba da shawarar gurfanar da El-Rufai a gaban kotu

Sai dai sanarwar ta ce dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin an dawo dasu Abuja cikin koshin lafiya, inda ta kara da cewa tikitin nasu ya ci gaba da aiki na tafiya a cikin makonni biyu.

Hukumar ta NRC ta kuma ba da hakuri kan wannan matsala da ta faru, tare da tabbatar da cewa ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron lafiyar fasinjojin ta.

Hukumar ta NRC, ta yi Allah wadai da barnar da aka yi, tare da lura da cewa tana kokarin ganin ba a sake samun irin wannan lamari ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here