
Masarautun Kano guda biyu masu hamayya sun sanar da dakatar da dukkan shirin hawan sallah na Babbar Sallah sakamakon matsalar tsaro da umarnin da hukumomin tsaro suka bayar dontabbatar da zaman lafiya a jihar.
A baya, duka Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, sun sanar da shirin gudanar da bukukuwan hawan sallah daban-daban a lokacin bukukuwan Sallar.
Duk da haka, yayin da yake sanar da dakatarwar a madadin Sarkin Kano Aminu Bayero, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, ya ce an ɗauki wannan hukuncin ne don bin umarnin ‘yan sanda don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
Ya ce su mutane ne masu bin doka kuma za su bi umarnin hukumomin tsaro gaba daya don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Haka kuma, yayin da yake magana a madadin Sarkin Kano na 16 Sunusi Lamido Sunusi, Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce majalisar masarautar ta samu rahotannin tsaro da ke nuna cewa wasu mutane na shirin amfani da bukukuwan bawan sallar wajen tayar da zaune tsaye da haifar da hargitsi a Kano.
A cewarsa, an yanke shawarar dakatar da ayyukan ne don gujewa duk wani karya doka da oda da kuma kiyaye yanayin zaman lafiya a jihar a lokacin bukukuwan sallar.
SolaceBase ta ruwaito cewa dakatar da hawan sallar na gargajiya ya zo ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali game da rigimar sarautar Kano.









































