NDC ta sanya ranar gudanar da zaben fidda gwanin shugaban kasa da na gwamna a fadin kasa

NDC NDC

Jam’iyyar NDC ta sanya ranar 29 ga Mayu 2026 don gudanar da zaben fidda gwanin shugaban kasa, gwamna, majalisar kasa da majalisun jihohi a fadin kasa.

Jam’iyyar ta ce shawarar ta biyo bayan cikas a harkokin sufuri da bikin Baabar Sallah da hutu suka haddasa, lamarin da ya shafi zirga-zirgar ‘yan takara da mambobin kwamitocin tantancewa a fadin kasa.

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Moses Cleopas, da sakataren jam’iyyar Barr. Ikenna Alex-Morgan Enekweizu suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce zaben fidda gwanin zai gudana ne daidai da tsarin lokaci da aka tsayar tun da farko na 28 da 29 ga Mayu.

A cewar sanarwar, 28 ga Mayu yanzu za a yi amfani da shi wajen isowa, yin rajista da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) da hukumomin tsaro, gudanar da tarukan shawarwari, da sauran ayyukan shiri gabanin zaben fidda gwanin.

Jam’iyyar ta bayyana cewa yawancin ‘yan takara da suka tafiAbuja don tantancewa, da kuma mambobin kungiyoyin tantancewa, sun makale a Babban Birnin Tarayya saboda matsalar sufuri da rashin samun jirage a wannan lokacin hutu.

“Ƙungiyoyin za su yi amfani da 28 ga Mayu wajen gudanar da taruka da masu ruwa da tsaki, dattawan jam’iyya, da kuma ‘yan takara a jihohinsu,” in ji sanarwar.

NDC ta kuma yi gargadin cewa babu wata hukumar tsaro ko gwamnati, ciki har da ‘Yan Sanda, INEC da Hukumar DSS, da ake tsammanin za ta halarci wani taro ko shiri da aka shirya a ranar 28 ga Mayu.

Ta bayyana cewa duk wani aiki da aka gudanar a wajen jagororin da aka amince da su za a dauke shi a matsayin mara izini kuma ba bisa ka’ida ba.

Jam’iyyar ta jera tsarin zaben fidda gwanin na 29 ga Mayu da suka hada da amincewa da dan takarar shugaban kasa, zaben fidda gwanin da amincewa da ‘yan takar majalisar kasa, zaben fidda gwanin da amincewa da ‘yan takararr majalisun jihohi, da kuma zaben fidda gwanin da amincewa da ‘yan takarar gwamna.

Ta kara da cewa duk sakamakon zabukan za a tattara kuma a aiwatar da su ta kwamitocin da aka ba alhakin kafin a mika su hedikwatar jam’iyyar ta kasa, inda Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) zai sanar da sakamakon bisa ka’ida.

NDC ta jaddada cewa babu wani zartarwa ko kungiya ta jiha da ke da hurumin sanar da sakamako.

Jam’iyyar ta kara roƙkn ‘yan takara da magoya bayansu da su nuna dabi’a cikin kwanciyar hankali, tana mai gargafin cewa ba ta yarda da tashin hankali, rudani da barna a lokacin zaben ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here