Za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Osun duk da shawarar Babban lauyan tarayya

Osun governor Ademola Adeleke 750x430

Gwamna jihar Osun Ademola Adeleke na Osun ya ce za a gudanar da zaben kananan hukumomin da aka shirya yi ranar Asabar.

Adeleke, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Osogbo, wanda mai magana da yawunsa Malam Olawale Rasheed ya rabawa manema labarai, ya bayyana haka a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar kungiyar hadin kan fararen hula.

Gwamnan wanda ya ce wakilan sun je jihar ne domin sanya ido kan zaben kananan hukumomin, ya kuma nuna jin dadinsa da irin shirye-shiryen da hukumar zaben jihar ta yi.

A cewar sa, masu zabe sun shirya yin amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a a ranar Asabar.

Karin labari: Babu wani dan siyasa mai hankali da zai koma APC-Tambuwal

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, a ranar Alhamis ya shawarci Adeleke da kada ya ci gaba da shirye shiryen gudanar da zaben.

Fagbemi ya bukaci gwamnan da ya mutunta kotun daukaka kara da ke Akure, hukuncin da ya mayar da shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar APC da kansiloli da babbar kotun tarayya a Osogbo ta kora a shekarar 2022.

Gwamnan ya shawarci dukkan bangarorin da suka hada da masu ruwa da tsaki na cikin gida da na kasa da su bi ka’idojin dimokuradiyya.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here