Babu wani dan siyasa mai hankali da zai koma APC-Tambuwal

Aminu Tambuwal 750x430

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce babu wani dan siyasa mai makoma da zai koma jam’iyyar APC.

Tambuwal yayi magana ne a ranar Asabar a Kaduna bayan taron majalisar zartarwa ta kasa na jam’iyyar PDP a shiyyar arewa maso yamma.

Tambuwal, wanda tsohon kakakin majalisar wakilai ne, ya ce halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki a halin yanzu ya sa duk wani wanda ya zama dan jam’iyyar APC mai mulki ba shi da kwarjini.

Karin labari: Babu wata madadin gwamnati da tafi ta APC – Masari

Ya lura cewa ‘yan siyasar da suka fice daga PDP suka koma APC “kayan aikin ciki ne ke jan hankalin su”.

Ya kara da cewa wadanda suka yi imani da kasar nan dole ne su hada kai domin ganin an kawar da gwamnatin APC a 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here