Jam’iyyar APC ta fitar da sabon jadawalin yadda za ta gudanar babban taronta na jihohi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Oktoba domin zaben shugabanninta.
Sakataren Jam’iyyar APC na rikon kwarya da kwamitin tsare -tsare na musamman (CECPC) Sanata John Akpanudoedehe ne, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja.
Yace wannan yazo daidai “da tanadi na kundin dokokin jam’iyar a sashi na ashirin da daya: Sashe na (i-xiii), da kuma na 17 (i).
“CECPC na babbar jam’iyyarmu ta amince da sake duba jadawalin ayyukan don gudanar da taronta a duk Jihohi a cikin tarayya don zaben jami’an jam’iyyar,” in ji shi.
A cewar Akpanudoedehe, siyan fom na takara a matakin Jiha wanda aka fara ranar Laraba (15 ga Satumba) zai ƙare a ranar Litinin (11 ga Oktoba), yayin da za a gudanar da tantance masu neman mukaman zartarwa na Jihohi a ranar 13 da 14 ga Oktoba.
Ya ce za a gudanar taron jihohin a ranar Asabar (16 ga Oktoba), yayin da za a shigar da korafe-korafe dangane da zaben daga ranar 23 ga Oktoba zuwa 30 ga Oktoba.
“A kan kudin fom na tsayawa takara, masu neman mukamin Shugaban jamiyar a matakin jiha za su sayi fom a kan N100,000. Mataimakin Shugaba da Sakatare da masu neman ma’aji za su biya N50,000.
“Masu neman kujerar Dattawa na jam’iyar za su sayi fom a kan N50,000; Shugaban Matasa N30,000 da sauran ofisoshi su ma N30,000.
‘Yan takara mata da masu bukata ta musamman za su biya kashi 50 na kudaden da aka kayyade ga kowane mukami, “in ji sakataren na APC.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa kwamitin rikon kwaryar na APC a taronta na 17 na ranar 29 ga Satumba, ta duba kuma ta amince da rahoton zabukan Kananan Hukumomi.
Kwamitin ya ba da tabbacin cewa zai yi nazari akan duk wani yanki da aka samun sabani.
Ta kuma ba da umarnin cewa za a gudanar da taron ta na Jiha a ranar 16 ga Oktoba a fadin tarayya, amma banda jihohin Zamfara da Anambra. (NAN)












































