Jami’ar Bayero ta haramta cajin ababen hawa masu amfani da lantarki a jami’ar

BUK BUK New

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta haramta cajinna babura da sauran motoci masu amfani da lantarki masu zaman kansu a harabar jami’ar.

Jami’ar ta sanar da wannan haramci ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar a ranar Talata.

SolaceBase ta rawaito jami’ar ta sanar kamar haka, “Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero, Kano ta lura da damuwa kan yadda ake cajin babura da sauran motocin lantarki masu zaman kansu ba bisa ka’ida ba ta hanyar amfani da wutar lantarkin Jami’ar a fadin harabarta.

‘Wannan dabi’a ta ba da gudummawa sosai wajen karuwar kudin wutar lantarkin da Jami’ar ke biya, lamarin da ya jefa jami’ar cikin babban nauyin kudi. A lokacin da Jami’ar ke kokarin yin amfani da albarkatu cikin hikima, ci gaba da amfani da wutar lantarkin Jami’a wajen cajin baburan lantarki masu zaman kansu a dakatar.

‘Saboda haka, Jami’ar ta haramta, daga yanzu, cajin babura da sauran motocin lantarki masu zaman kansu a dukkan harabobin Jami’ar.

‘Dangane da haka, dukkan ma’aikata, dalibai, masu sana’ar kabu-kabu da sauran masu amfani da ababen hawa masu amfani da lantarki ana umartarsu su daina cajin babura ta hanyar amfani da wutar lantarkin Jami’ar.

‘Jami’ar tana sa ran a bi wannan umarni cikin cikakkiyar biyayya. Duk wanda aka samu ya karya wannan haramci zai fuskanci matakin da ya dace bisa ka’ida da dokokin Jami’ar.

A cewar sanarwar, domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata, ana rokon duk Provosts, Deans, Directors, Shugabannin Sassa da Shugabannin Bangarori su sanya ido kan yadda ake bin wannan umarnin a bangaren da suke da alhaki, su kuma ba da rahoton hakan ga hukumomin da suka dace.

Bugu da kari, Za a kafa tawagar sanya ido na Jami’ar da za ta rika sintiri a dukkan harabobin domin tabbatar da bin umarnin.

Saboda haka ana bukatar duk wadanda lamarin ya shafa su dauki wannan umarni da muhimmancin da ya dace, tare da baiwa Jami’ar hadin kai wajen rage kudin makamashi da tabbatar da yin amfani da albarkatunta yadda ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here