Mun biya Naira miliyan 50 don kubutar da alkalin Kebbi – Inji iyalansa

Justice Faruku Hassan Bunza of the Kebbi State High Court 1

Iyalan alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruk Hassan Bunza, da aka yi garkuwa da shi a gidansa, sun tabbatar da cewa sun biya Naira miliyan 50 domin kubutar da shi.

An yi garkuwa da Mai Shari’a Bunza da sanyin safiyar ranar Lahadi, 26 ga Yuli, lokacin da ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai hari gidansa da ke Karamar Hukumar Bunza ta Jihar Kebbi.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi garkuwa da alkalin da ke aiki a kasar nan a kwanakin baya, bayan an yi garkuwa da alkalin Babbar Kotun Jihar Bayelsa, Ebiyerin Umokoro, a watan Yunin 2025.

Mai Shari’a Bunza ya shaki iskar ‘yanci a ranar Litinin bayan ya shafe kwanaki 8 a hannun masu garkuwar.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, iyalinsa da Ma’aikatar Shari’a ta jihar ne suka tabbatar da sakin nasa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bashir Usman, ya ce a cikin wata sanarwa cewa an sake alkalin da sanyin safiyar Litinin kuma ya hadu da iyalinsa cikin koshin lafiya.

“Yanzu da aka sake alkalin, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kara kaimi domin bincike don gano wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su,” in ji sanarwar.

Kwamandan ya kuma gode wa jama’a da sauran hukumomin tsaro kan goyon bayan da suka bayar a lokacin aikin.

Ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da bada bayanan sirri da zasu taimaka wa jami’an tsaro wajen kama masu garkuwar.

Wani daga cikin iyalin Mai Shari’a Bunza, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya shaida wa Daily Trust cewa an biya Naira miliyan 50 ga masu garkuwar.
Ya ce yanzu ana kula da alkalin kuma yana samun sauki a gidansa da ke Bunza.

A cewar dan iyalin, masu garkuwar da farko sun nemi Naira miliyan 200 amma daga baya suka amince da Naira miliyan 50 bayan shafe kwanaki ana tattaunawa a tsawon lokacin da alkalin ke hannunsu.

“Muna ci gaba da kula da shi a gida tun bayan sakin sa a ranar Litinin. Kamar yadda kuka sani, yana bukatar lokaci domin ya warke daga abin da ya fuskanta.

Za mu yi magana da manema labarai idan ya warke gaba daya, sannan za mu ba da cikakken bayanin abin da ya faru a hannun masu garkuwar. Amma kan batun an biya kudin fansa ko a’a, na iya tabbatar muku cewa an biya Naira miliyan 50,” in ji majiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here