Tinubu ya sabunta wa’adin Manajan Daraktan NAN da Darakta Janar na NTA

Bola Tinubu signs 750x430 (1)

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sabunta wa’adin Malam Ali Muhammed Ali, Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai ta Kasa (NAN), na shekaru uku.

Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Onanuga ya ce Shugaban Kasar ya kuma sabunta wa’adin Darakta Janar na Hukumar Talabijin ta Kasa (NTA), Malam Abdulhamid Dembos.

Ya bayyana cewa Shugaban Kasar  ya fara nada Dembos na NTA da Ali na NAN a ranar 20 ga Oktoba 2023, inda ya kara da cewa wa’adin su na biyu zai fara ne a ranar 20 ga Oktoba 2026.

Onanuga ya kara da cewa Dembos dan asalin Jihar Adamawa ne, kuma tsohon Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin, Gidan Wasanni da Fasaha (RATTAWU) ne.

Ya kuma kara dace Dembos ya taba zama Daraktan Tallace-Tallace a NTA bayan ya yi ritaya a shekarar 2017.

A cewarsa, Dembos ya fara aiki a NTA a matsayin mai karanta labarai a tashar Kaduna bayan kammala shirin hidimar kasa (NYSC)a shekarar 1989.

“Ya ci gaba da rike mukamai daban-daban. A lokuta da dama ya yi aiki a matsayin Babban Manaja na NTA a Lokoja da NTA Kano. Ya yi ritaya ne a matsayin Mukaddashin Darakta na Yanki, NTA Kaduna, a shekarar 2017.”

Onanuga ya ce Ali Muhammed Ali gogaggen dan jarida ne, manajan gidajen jaridu da ya yi aiki sama da shekaru 30.

“Ya samu digirin farko a fannin Turanci daga Jami’ar Bayero dake Kano. Har ila yau yana da digirin biyu a fannin Harkokin Kasa da Kasa daga Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, da kuma Difloma ta Kwarewa a fannin aikin jarida daga Jami’ar Bayero, Kano.”

Onanuga ya ce Tinubu ya bukaci manyan jami’an biyu da su tabbatar da amincewar da aka ba su ta hanyar ci gaba da nuna himma wajen cika ayyukan hukumar su da kuma inganta Shirin Sabunta Fatan Al’umma na gwamnati. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here