Yobe: An cafke matasa 60 da ake zargi da shan miyagun Ƙwayoyi

Drug Abuse in Yobe 750x430

Akalla mutane 60 aka cafke wadanda ake zarginsu da hannu a wani samame na hadin gwiwa da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Babban jami’in gwamnatin jihar kan hana shan miyagun kwayoyi, Malam Saidu Jakusko, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da ya ke zanta wa da manema labarai a birnin Damaturu.

Jakusko ya ce, aikin hadin guiwan wanda ya hada da ‘yan kungiyar sanya Ido da kuma jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ya kai ga cafke maza 30 da mata 30.

Ya bayyana cewa, matakin ya zama dole ne biyo bayan yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa a jihar.

Jakusko, ya kara da cewa, galibin wadanda ake zargin suna wajen wani ruwa ne a daidai lokacin da aka kama su, kuma daga cikin su akwai wasu mashahuran dilolin miyagun kwayoyi guda uku wadanda suka kasance cikin jerin sunayen mutanen da jami’an tsaro ke nema Ruwa a Jallo.

Ya ce, ana kan tantance mutanen da aka kama, kuma za a mayar da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne zuwa jihohinsu.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sheikh Abubakar Muhammad, wanda aka gayyace shi domin yi wa wadanda ake zargin nasiha kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, ya gargade su da su ji tsoron Allah su tafiyar da rayuwarsu ta hanyar da tadace.

Sheikh Muhammad, ya koka da cewa, wadanda ake zargin galibinsu matasa ne da ya kamata su kasance masu amfani a cikin al’umma.

Haka kuma yayi kira ga iyaye da su rika lura da yayansu tare da tabbatar da cewa ba su shiga cikin bata gari ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here