Sarkin Gusau Ibrahim Bello ya rasu ya na da shekaru 71

Emir of Gusau Ibrahim Bello 720x430

Sarkin Gusau Ibrahim Bello, ya rasu ya na da shekaru 71 a duniya.

Sarkin ya rasu ne da safiyar yau Juma’a a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya fitar yau Juma’a, inda ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi.

Sanarwar ta ce, Sarkin ya kasance Uba ne mai goyon bayan sarauta wanda ke aiki tuƙuru domin ci gaban jihar.

“Na samu da bakin ciki matuka game da rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, Sarkin Gusau,” in ji sanarwar.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa, za a yi jana’izar sarkin na Gusau a yau Juma’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here