Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi bakuncin tawagar daga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da kuma kamfanin gini na Mota-Engil Nigeria gabanin bikin kaddamar da aikin Jirgin Kasa na Kano wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi kwanan nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Tawagar karkashin jagorancin Dr. Armstrong Ume Takang na Ma’aikatar Kudin da Shugaban Mota-Engil Nigeria, Kola Karim, sun gana da Gwamna a Gidan Gwamnan Jihar Kano da ke Asokoro, Abuja, domin sanar da shi matakin da shirye-shiryen fara aikin suka kai.
A cewar sanarwar, aikin Jirgin Kasa na Kano da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi da kudin kwangila na Naira tiriliyan 1.05, ana sa ran zai samar da sauyi a bangarn sufuri a cikin birnin Kano, inganta hanyoyin sadarwa, rage cunkoson ababen hawa da kuma bunkasa harkokin tattalin arziki a fadin jihar.
Gwamna Yusuf ya tarbi tawagar kuma ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Jihar Kano na aiki tare da Gwamnatin Tarayya da masu yin kwangilar aikin domin tabbatar da nasarar wannan babban aikin.
Ya bayyana shirin aikin jirgin kasa a matsayin zuba jari mai muhimmanci da zai karfafa matsayin Kano na cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya, tare da bai wa al’umma tsarin sufuri na zamani, mai aminci da inganci.
Gwamna Yusuf ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa zabar Kano ta amfana da wannan gagarumin aiki.
Haka kuma ya mika godiya ta musamman ga Hon. Abubakar Kabir Bichi, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Raba Kudi, bisa goyon bayan doka da ya bayar wajen gudanar da aikin.













































