Matakin Gwamnatin Tarayya na yin garambawul ga hukumar dake kula da masu yi wa kasa hidima ta NYSC na daga cikin manyan sauye-sauye da aka yi wa tsarin tun sama da shekaru hamsin da suka gabata. Amma ga yawancin ‘yan Najeriya, tambayar da ke da muhimmanci ba ita ce ko ana bukatar gyaran bane, sai ko sabbin sauye-sauyen za su magance matsalolin na hakika da tsarin yake fuskanta.
An kafa NYSC ne da dokar lamba 24 ta 22 ga Mayu 1973, a karkashin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon, a matsayin wani shiri na bayan yakin Basasa don sake gina kasa mai rarrabuwar kai. Bayan yakin Basasar Najeriya a 1967 zuwa 1970, kasar ta bukaci wani tsari da zai inganta sulhu, hadin kan kasa, hada al’adu da kuma amfani da matasan da suka yi karatu wajen bunkasa kasa.
Bayan sama da shekaru hamsin da suka wuce, NYSC na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan cibiyoyi a Najeriya. Miliyoyin masu digiri sun shiga shirin, suna hidima a makarantu, asibitoci, hukumomin gwamnati, al’ummomin kauye da kamfanoni masu zaman kansu a fadin kasar.
Ba za a iya musanta nasarorin da tsarin ya samu ba, ya hada matasan Najeriya da al’adu daban da ba nasu ba, ya karfafa fahimtar juna tsakanin kabilu, ya inganta hadin kan kasa, ya samar da kwarru a wuraren da ake bukata, ya inganta lafiya da ilimi a kauyuka, kuma ya samar da dubban ‘yan kasuwa ta hanyar shirin koyon sana’a da bunkasa ‘yan kasuwa (SAED). Hadin da ya hada kabilu da abokantaka da ta dade ma sun samo asali ne daga tsarin, wanda ya kara karfafa hadin kan kasa.
Amma duk da wadannan nasarorin, NYSC a yanzu na fuskantar mafi girman jarabawa tun kafa shi.
Tsaro ya zama babbar matsala. A ‘yan shekarun nan, ‘yan kasa sun zama abin sace-sace, hare-hare, rikicin al’umma da hatsarin mota a wuraren hidima da ba su saba ba. Yanzu iyaye da yawa suna jin tsoron aika ‘ya’yansu zuwa wasu sassan kasar.
Wata matsalar kuma ita ce karancin samar da walwala. Ko da yake an kara alawus din wata-wata, ‘yan kasa da yawa har yanzu suna fama da tsadar sufuri, masauki da rayuwa. A wasu jihohi, masaukin da aka yi alkawari ko babu shi ko kuma yana cikin halin da ba za a zama ba.
Matsalar samar da daidaito a tsakanin abin da dalibi ya karanta da wurin aikin da aka tura shi, ma yana damun mutane. Ana tura injiniyoyi su yi aikin ofis, yayin da wasu da ke da wata kwarewa a fannoni ma sukan samu kansu ba tare da an amfani da su yadda ya kamata ba. Wannan ya saba wa manufar amfani da kwararrun kasa.
Shirin kuma yana fama da rashin kayayyakin aiki a sansani, raunin sanya ido kan ma’aikata, cin hanci a wurin tura mutane, rashin kayayyakin duba lafiya a sansani da kuma rashin goyon baya bayan kammala hidima.
Wadannan dalilai ne suka sa ‘yan Najeriya suka dade suna neman cikakken garambawul.
Da yawa sun nemi a inganta tsaro ta hanyar tura mutane bisa bayanai, domin kada a tura masu digiri zuwa yankunan da ake fama rikici. Wasu sun ba da shawarar a sanya shirin na zabi ba tilas ba, yayin da wasu suka ce a tura mutane yankinsu don rage hadari.
Wata babbar bukata kuma ita ce a daidaita aiki da karatun mutum. ‘Yan Najeriya suna sa ran samun ingantaccen masauki, inshorar lafiya, kara alawus din da ya dace da tsadar rayuwa, ba da tallafin fara sana’a bayan hidima, sauya tsarin NYSC zuwa na zamani, da hadi kai da masana’antu don samun aiki.
Har ma an yi kira da a gyara kundin tsarin mulki da dokoki domin a sake fayyace manufofin tsarin bisa yanayin Najeriya ta yau, ba ta 1973 ba.
A gefe guda, Gwamnatin Tarayya ta amince da manyan gyare-gyare. Daga cikinsu akwai sanya shugabancin farar hula maimakon na soja, tsarin gayyata da ke amfani da fasaha, tura mutane bisa tsaro, kara tsawon zaman sansani daga makonni 3 zuwa 6, kara maida hankali kan sana’a da fasahar zamani, raba masu digiri bisa fannin karatunsu, inganta sansani, sauya riguna, yin bikin kammala karatu maimakon baje kolin karshe, da gyara dokar NYSC.
Wadannan gyare-gyaren su ne mafi girma tun kafa tsarin. Sun nuna cewa gwamnati ta fahimci bukatar mayar da NYSC zuwa tsarin karni na 21.
Amma duk da haka, gyare-gyaren ba su amsa dukkan tambayoyin ‘yan Najeriya ba.
Ko da yake kara tsawon zaman sansani da sauya riguna na iya inganta tsarin, ba za su warware manyan matsaloli na rashin tsaro, rashin aiki da samar da walwala ba. Nasarar kowane gyara zai dogara ne kan yadda za a aiwatar da shi, ba kawai sanarwa ba.
Tsaro ya rage shi ne babban damuwa. Ba tare da ingantattun bayanai, aiki tare da hukumomin tsaro da guje wa wurare masu hadari ba, rayuwar ‘yan kasa za ta ci gaba da kasancewa cikin hadari.
Hakazalika, horon sana’a ba zai yi tasiri ba sai idan masu digiri sun samu kudin rance mai sauki, koyarwa, kasuwa da goyon baya bayan kammala hidima.
Ya kamata gwamnati ta tabbatar cewa kowane dan kasa ya samu aiki da ya dace da karatunsa ko sana’arsa. Shirin ya kamata ya zama gada tsakanin jami’a da samun aiki mai ma’ana, ba kawai shekara guda ta tilas ba.
Akwai bukatar a kara duba ga ma’aikata bisa aiki, sanya ido kan jin dadin ‘yan kasa, tilasta inshora, sa ido da fasaha kan tura mutane da halarta, inganta sansani, tantance wuraren aiki lokaci zuwa lokaci, da hada kai da kamfanoni masu zaman kansu da za su iya daukar ‘yan kasa bayan hidima.
Ya kamata NYSC ta kafa Asusun Tallafi don tallafawa kasuwanci da aka samar a lokacin hidima, wannan zai canza tsarin daga na hadin kai kawai zuwa na bunkasa tattalin arziki.
Abu mafi muhimmanci, Gwamnatin Tarayya ya kamata ta sanya yin bita mai zaman kansa na NYSC duk bayan shekaru biyar domin tsarin ya ci gaba da dacewa da yanayin kasa.
NYSC na daga cikin manyan gwaje-gwajen gina kasa. Manufar kafa shi ta hadin kan kasa har yanzu tana da mahimmanci a kasar da rarrabuwar kabilu, addini da yankuna ke barazana ga hadin kai.
Amma son kasa kadai ba zai iya daukar tsarin ba. Matasan Najeriya sun cancanci shirin da ke tabbatar da tsaronsu, bunkasa basira, shirya su don aiki, ba su lada, da kuma taimaka wa ci gaban kasa.
Gyare-gyaren yanzu mataki ne mai kyau, amma mataki na farko ne kawai. Abin da ‘yan Najeriya suke so ba kawai NYSC ta zamani ba, sai dai wata cibiya da ta canza wadda za ta kare rayuka, samar da dama, ƙarfafarmaki hadin kan kasa da kuma shirya kowane dan kasa don ba da gudunmawa ga makomar Najeriya.
Idan haka ta faru, to burin Janar Yakubu Gowon na 1973 zai cika a bisa burin sabon tsar ‘yan Najeriya.













































