Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kashe fiye da Naira biliyan 996.29 kan ayyuka 1,557 a fadin ƙananan hukumomi 44 na jihar a cikin shekaru uku da suka gabata.
Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyuka, Sanya Ido da Tantancewa na Jihar, Hon. Nura Iro Ma’aji, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Kano.
Ma’aji ya ce ayyukan da ake kimantawa a halin yanzu sun kai darajar fiye da Naira biliyan 695, wanda hakan ke wakiltar kusan kashi 70 cikin dari na jimillar darajar ayyukan.
Ya bayyana cewa ma’aikatar, a cikin wannan lokaci, ta tantance bukatun biyan kudin ‘yan kwangila da suka kai Naira biliyan 444.75 na ayyukan da suka gudanar.
“A cikin shekaru uku da suka gabata na wannan gwamnati, mun tantance fiye da Naira biliyan 444 na ‘yan kwangila don ayyukan da suka yi,” in ji shi.
A cewar kwamishinan, ayyuka 867, wadanda ke wakiltar kashi 55 cikin dari na jimillar ayyukan, an kammala su, yayin da ayyuka 654 dake wakiltar kashi 42 cikin dari, suna ci gaba da gudana.
Ya kara da cewa ayyuka 26, masu wakiltar kashi 1.66 cikin dari, suna matakin amincewa, yayin da ayyuka 10 ke karkashin tantancewa don amincewa.
Ma’aji ya bayyana cewa an raba ayyukan guda 1,557 zuwa manyan rukunoni guda uku bisa ga fadin yankunan da suka shafa,ayyukan da ke cikin karamar hukuma daya, ayyukan da suka shafi kananan hukumomi fiye da daya da kuma ayyukan da suka shafi duka kananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce ana gudanar da ayyuka 598 a cikin kananan hukumomi takwas na cikin birnin Kano da suka hada da Dala, Fagge, Kano Municipal, Kumbotso, Tarauni, Nassarawa, Ungogo, da Gwale akan jimillar kudi Naira biliyan 299.36 biliyan, wanda ke wakiltar kashi 30 cikin dari na jimillar darajar ayyukan.
Kwamishinan ya ce kananan hukumomi 36 na wajen birni suna da ayyuka 653 darajarsu ta kai Naira biliyan 283.90, wanda ke wakiltar kashi 28 cikin dari na jimillar darajar ayyukan.
Ya kara da cewa ana aiwatar da ayyuka 37 a fadin kananan hukumomi fiye da biyu da darajarsu ta kai Naira biliyan 159.50, wanda ke wakiltar kashi 16 cikin dari.
“Ayyukan da suka shafi daukacin ƙananan hukumomi 44 sun kai ayyuka 269 da darajaru ta kai Naira biliyan 249.54, wanda ke wakiltar kashi 25 cikin dari na jimillar darajar ayyukan.”
Ma’aji ya kuma kara da cewa ayyukan da suka shafi daukacin jihar sun hada da fitulun titi, fitulun ababan hawa na hasken rana (wireless solar traffic lights), tsarin kula da ababan hawa da fitulun ababan hawa da kuma manyan ayyukan hanyoyi.
“Daga cikin ayyukan hanyoyin akwai hanyar Dakata-Yadakunya, Janguza-Rurum, Kabo-Karaye, da hanyoyin Madobi-Kwanar Dangora da dai sauransu.”
Haka kuma ya bayyana rukunin gidajen Rijiyar Gwamgwan a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin ke aiwatarwa, wanda aka kiyasta zai ci Naira biliyan 113.19.
Kwamishinan ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan abin da ya bayyana a matsayin kokarin habaka ci gaba a fadin jihar, musamman a bangaren ababen more rayuwa.
Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da nufin inganta rayuwar al’umma a fadin Jihar Kano.
Ma’aji ya yi kira ga jama’a da su marawa gwamnati da ma’aikatar baya, tare da ba su tabbacin cewa ma’aikatar za ta ci gaba da sanya ido kan yadda ake amfani da kudaden gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan gwamnati.













































