Shekara 85: Babu shugaban da ya yi tasiri a Najeriya kamar Babangida – Tinubu

IBB with Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon Shugaban Kasar Soja, Janar Ibrahim Babangida Mai Ritaya, murnar cika shekaru 85, inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen shugaban Najeriya.

Tinubu ya ce kyakkyawan aikin sojan Babangida ya kai ga ya zama shugaban kasa bayan juyin mulkin 1985.

Wannan na cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Shugaban ya ce Babangida ya yi tasiri sosai a Najeriya, inda ya bar alamomi da za su dore a fannin siyasa, tattalin arziki da yanayin kasar.

“Ko kuna sonsa ko ba ku sonsa ba, tsohon Shugaba Babangida ya yi tasiri a Najeriya fiye da kowane shugaba. Mulkinsa na shekaru takwas ya bar alamomin da zasu dore a siyasarmu, tattalin arzikinmu da tsarin kasarmu,” in ji Tinubu.

Ya ce Babangida ya fadada tattalin arzikin Najeriya, ya samar da ababen more rayuwa masu dorewa, kuma ya kafa hukumomi da cibiyoyi da ke ci gaba da hidimtawa kasar.

“Badan hangen nesa, hikima, adalci da gaskiya ba irin nasa ba, da mafi yawan jihohin da ake da su a cikin tarayya Najeriya babu su a yau,” in ji Shugaban.

Tinubu ya ce sunan Babangida da hidimarsa za su ci gaba da kasancewa a tarihin Najeriya saboda gudummawar da ya bayar wajen cigaban kasa.

Shugaban ya kuma yaba da ci gaba da gudummawar da Babangida ke bayarwa wajen tattaunawa kan al’amuran kasa, duk da cewa ya yi ritaya daga harkokin gwamnati.

“Ko da yake ya yi ritaya, yana rayuwa cikin nutsuwa a gidansa na Hilltop da ke Minna a Jihar Neja, Janar Babangida na ci gaba da ba da shawara da jagoranci mai amfani ga kasar.
Shawarwarinsa da hikimarsa na ci gaba da zama abin koyi ga tsararraki masu tasowa.”

Shugaban ya yi wa tsohon shugaban sojan fatan samun lafiya, karfi da karin shekaru don hidima ga kasa.

“Ina yi maka fatan alheri, lafiya mai kyau, da sabon karfi. Allah Madaukakin Sarki ya bar mu da kai na shekaru masu yawa masu zuwa,” in ji Tinubu. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here