Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ba da umarnin a saukar da tutocin Amurka a fadin kasar tsawon mako guda domin girmama gwarzuwar wakar kasa, Dolly Parton, bayan rasuwar ta tana da shekara 80.
Trump ya yabi wannan fitacciyar jarumar waka da ta rasu, inda ya bayyana rasuwar ta a matsayin babban rashi ga miliyoyin mutane.
“Wannan babban rashi ne ga miliyoyin mutane. Ba a taba samun wanda ya yi kama da ita ba, kuma ba za a samu ba… Hutawa Lafiya, Dolly! Duniya tana son ki,” in ji Trump.
Wannan mataki ya biyo bayan rasuwar Parton a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, tana da shekara 80.
Parton na daga cikin shahararrun mutane a fannin wakar kasar, inda ta shafe sama da shekaru sittin tana yin waka.
An san ta da manyan wakoki irin su “Jolene,” “Coat of Many Colours” da “I Will Always Love You,” yayin da aikinta ya kuma shafi wasan kwaikwayo, kasuwanci da aikin taimakon jama’a.
Wakar ta “I Will Always Love You” ta kara samun karbuwa a duniya bayan Whitney Houston ta rera ta a fim din 1992 mai suna The Bodyguard.
Parton ta kuma kafa Dolly Parton Imagination Library, wani shiri da ke ba da littattafai kyauta ga kananan yara.
Ana ci gaba da alhinin mutuwarta daga magoya bayanta da manyan mutane, inda da yawa suke tunawa da gudummawar ta ga waka da ayyukan taimako.
BBC













































