Daraktocin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) na shiyyar Arewa maso Yamma sun yi kira da a karfafa yada bayanan sirri da hadin gwiwar ayyuka domin murkushe ta’addanci, fashi dajin da sauran barazanar tsaro a yankin.
Sun yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin taron Daraktocin Tsaro na Jihohin Arewa maso Yamma (SDS) da hukumar DSS ta shirya a jihar Katsina, mai taken: “Mu Hadu Waje Guda Don Yakar Ta’addanci.”
Babban daraktan tsaro na jihar Katsina, Alhaji Alhassan Iliyasu, ya bayyana cewa taron ya ba wa hukumomin tsaro damar duba sabbin kalubalen tsaro da kuma fito da dabarun hadin gwiwa don magance su, inda ya kara da cewa taron zai ba mahalarta damar musayar gogewa, gano rabe-raben dake akwai da kuma karfafa dabarun yakar fashi da makami da sauran laifuka. Abubuwan da aka tattauna za su haifar da sanarwa ta hadin gwiwa wadda za ta zama jagorar aiki ga hukumomin tsaro a yankin.
A cewarsa, yaki da ta’addanci yana bukatar sa hannun kowa da kowa, ciki har da hukumomin tsaro, al’ummomi, kungiyoyin sa-kai da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro a Katsina, inda ya ce hakan ya taimaka kwarai wajen inganta tsaro a jihar. Kazalika, ya jaddada cewa shigar da rundunar tsaron al’umma ta da kungiyoyin sa-kai ya karfafa fafutukar da ake yi a fagen fama, kuma ya yi kira ga mazauna yankin da su rika kai rahoton duk wani motsi na zargi ga hukumomin tsaro.
Yayin da yake jawabi, Kwamandan Birgediya ta 17, Janar Ishaya Ibrahim, ya bayyana taken taron a matsayin wanda ya dace da lokaci, ya bayyana cewa, ko da yake karfin soja da dabarun yaki suna da mahimmanci, sahihan bayanan sirri su ne babban jigo wajen tabbatar da nasarar ayyukan yaki da ta’addanci.
Ya yaba wa hukumar DSS kan ayyukanta na tattara bayanan sirri, sa ido da dabarun al’umma, wadanda ke taimaka wa sojoji wajen kai samame cikin nasara. Ya ce ‘yan ta’adda na amfani da rabe-raben sadarwa da rashin amana don haka dole ne hukumomi su toshe wadannan kofofi ta hanyar raba bayanai a take da kuma gudanar da taron horaswa na hadin gwiwa.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, wanda Mataimakinsa Faruk Lawal-Jobe ya wakilta, ya yaba wa hukumar DSS kan shirya wannan taro, inda ya bayyana cewa kalubalen tsaro na yankin suna da alaka da juna, saboda haka suna bukatar tsari iri daya da kuma dorewar hadin gwiwa.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar Katsina ta samu gagarumar nasara ta hanyar amfani da dabarun soja da na zaman lafiya. Bugu da kari, gwamnati na aiwatar da shirye-shirye don inganta rayuwar al’ummomin da fashi ya shafa, kamar ba da magani kyauta ga wadanda harbin bindiga ya shafa, da kuma tallafa wa harkar noma ta hanyar samar da injuna, ingantattun irrai, da takin zamani.













































