An sada jaririn da aka sace a Asibitin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ga Iyayensa

ATBUTH
ATBUTH

Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi, ta ce an samu nasarar ceto wani jarirai Dan tagwaye, mai kwanaki 14 da aka sace a asibitin.

Dakta Haruna Liman, Shugaban Kwamitin Ba da Shawarwari ga Likitoci (CMAC) na asibitin shi ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake mika jaririn ga mahaifiyarsu ranar Talata a Bauchi.

Ya ce an sace jaririn daga hannun mahaifiyarsa a asibiti bayan kwana takwas da haihuwarsu.

“An sace jaririn ne a ranar 21 ga Satumba, 2022 da karfe 4:30 na yamma daga hannun mahaifiyarsa da ke karbar magani a asibiti.

Dakta Liman ya ce tuni jami’an tsaro suka cafke wata mata da ake zargi da kitsa wannan mugunyar dabi’ar.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar gudanarwa Asibitin za ta yi nazari kan tsarin tsaro na asibitin tare da sanya karin na’urorin fasahar tsaro a asibitin.

Hakimin Bauchi, Alhaji Nura Jumba, ya bukaci mahukuntan asibitin da su sake duba tsarin tsaron asibitin domin gujewa sake aukuwar irin haka anan gaba.

Ya yi alkawarin cewa a ko da yaushe shugabannin gargajiya za su ci gaba da wayar da kan al’umma kan lokutan da suka dace a ziyarci marasa lafiya a asibiti.

Jumba ya Kuma bukaci mahukuntan da su kulla alaka da iyali, da nufin ganin sun fahimci halin da suke ciki.

Da yake mayar da martani a madadin iyalan jaririn, Malam Shitu Kalid ya bayyana jin dadinsa ga mahukuntan asibitin bisa damuwar da suka nuna da kuma namijin kokarin da jami’an tsaro suka yi kan ceto jaririn.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here